“Shin Wannan Danki Ne”: Martanin Jama’a Bayan Ganin Matar Wada Na Yi Masa Shirin Zuwa Makaranta

“Shin Wannan Danki Ne”: Martanin Jama’a Bayan Ganin Matar Wada Na Yi Masa Shirin Zuwa Makaranta

  • Wata matar da ta auri wada mai karamin halitta ta yadu a kafar sada zumunta, jama’a sun yi martani game da rayuwarsu
  • A cikin wata bidiyon da muka gani a TikTok, ga matar na shirya mijin nata yayin da zai tafi aiki, tana shafa masa mai da sanya masa takalmi
  • A lokaci da aka yada bidiyon, ya dauki hankalin mutane da yawa, wasu na tambayar ya matar za ta yi idan ta haifi wadanni

Wata mata da mijinta wada sun dauki hankalijn jama’a a kafar TikTok ganin yadda matar ke ba mijinta kyakkyawar kulawa.

A bidiyon da aka yada a TikTok a ranar 3 ga watan Mayu, ya nuna lokacin da matar ke shirya mijinta da safe sadda zai tafi aiki.

Ya kuma nuna matar mai suna Patience da mijinta a cikin dakinsu da sanyin safiya lokacin da suke shirin ranan da ayyukan gida.

Kara karanta wannan

“Ba Zan Yafewa Mahaifiyata Ba”: Matashiya Ta Caccaki Mahaifiyarta Cikin Hawaye, Ta Ce Tana Kokarin Kashe Mata Aure

Matar wada da ke ririta shi ta ba da mamaki
Hotunan yadda matar wada ke ririta mijinta | Hoto: patience...dk
Asali: TikTok

Matar wada ta fadi rayuwarsu

A muryar matar da aka ji a cikin bidiyon, ta ce mijinta yakan nemi ta yi masa tausa kafin ya tafi wurin aikinsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta ce ta kan yi amfani da damar wajen shafa masa mai a jikinsa dakansa sannan ya sanya masa sutura kamar dai karamin yaron da zai tafi makaranta.

Patience ta kuma hada ma mijinta karin kumallo mai kyau, inda ta kawo masa ruwa cikin mutuntawa don ya wanke hannunsa ya ci tuwo.

Ganin yadda take tarairayarsa, mutane da yawa na ta mamakin yadda take masa abu kamar wani danta.

Legit.ng ta tattauna da Patience, inda ta tabbatar mana cewa mijinta ne kuma sunansa Derrick wanda tace malamin makaranta ne.

Kalli bidiyon da @patience...dk ta yada:

Martanin jama’a daga kafar TikTok

@Rawuda Sheriff:

Kara karanta wannan

“Wayyo Allah Ni Cokali Ce?” Bidiyon Kyautar Tsaleliyar Mota Da Saurayi Ya Yi Wa Budurwarsa Ya Dauka Hankali

“Jama’a ku kwantar da hankali makaranta zai iya zama jama’a ko masta.”

@ejikeokei:

“Shin wannan mijinki ne ko danki?"

@Irine Bara:

“Allah ya albarkaci aurenku. Ahali mai ban sha’awa.”

@Enow makanaki:

“Allah madaukaki ya ci gaba da sanya albarka a ahalinku.”

@fonfaithfon:

“Bari na bibiye ku don na ci gaba da samun labaran soyayyarku.”

@zino_rita:

“Akalla dai tana cikin farin ciki kuma hankalinta a kwance.”

@Nikkie:

“Shin wannan danki ne?”

@Carister perfect touch:

“Soyayya wata kyakkyawar aba ce.”

Wata yarinyar da ta rubuta jarrabawar JAMB ta bayyana bacin rai yayin da ta duba, ta ga ta ci 259.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.