Ganduje Ya Ba Da Kyautar Gida Da Miliyan N3 Ga Yar Kano Da Ta Zo Ta Biyu a Gasar Karatun Al-Qur’ani Na Duniya
- Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi wa yar jihar da ta zo ta biyu a gasar Al-Qur'ani na duniya sha tara ta arziki
- Ganduje ya ba wa Aisha Abubakar Dorayi kyautar gida da tsabar kudi har naira miliyan 3
- A cewarsa an yi hakan ne domin karfafawa sauran al'ummar jihar gwiwa tare da zaburar da su
Kano - Gwamnatin Jihar Kano ta yi alkawarin bayar da sabon kerarren gida da naira miliyan 3 ga yar asalin jihar, Aisha Abubakar Dorayi, saboda zuwa ta biyu da ta yi a gasar karatun Al-Qur'ani na duniya, wanda aka yi a kasar Dubai.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi alkawarin ne yayin taron majalisar zartarwa na jihar wanda ya gudana a gidan gwamnatin Kano, Daily Trust ta rahoto.

Source: UGC
Dalilin da yasa muka yi wa yarinyar kyauta, Ganduje
Ya ce an yanke shawarar bata kyautar ne domin karfafawa sauran yan jihar gwiwar jajircewa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ganduje ya ce:
"Wannan nasarar ba na Aisha bace ita kadai, ba na iyayenta bane su kadai, na jihar Kano ne. Wannan ne dalilin da yasa muka yanke shawarar zaburar da ita da kyautar gida a cikin sabbin gidajen da aka ginawa malamai a jihar. Mun kuma yanke shawarar ba yarinyar tsabar kudi naira miliyan 3. Muna alfahari da ita."
Da yake jawabi bayan sanarwar, wacce aka karrama, Aisha Abubakar Dorayi daga karamar hukumar Gwale ta jihar ta yaba da wannan karamci da aka yi mata sannan ta yi alkawarin ci gaba da zage damtse.
Ta yabawa iyayenta, malamai da abokan karatunta da ke karkafa mata gwiwa wajen samun ilimi har zuwa wannan matakin.
Ta ce:
"Ina farin ciki a yau da gwamnatin jihar ta lura da wannan nasarar. Amma nasarar namu ne mu dukka, musamman malamai da iyayena. Sun tsaya ka'in da na'in tare da ni don cimma wannan a yau. Ba zan iya gode masu ba. Allah ya saka masu da alkhairi dukka."
Bidiyon mahaukaci da ke tsafiya mai nisa don daukar daraji a jami'ar Benin ya dauka hankali
A wani labarin, wani matashi mai lalurar tabin hankali ya ja hankalin mutane da dama a soshiyal midiya bayan cin karo da bidiyonsa zaune a cikin jami'ar Benin.
A tunaninsa, matashin ya ce yana zuwa daukar darasi ne domin dai a kan gano shi zaune da takarda da biro.
Asali: Legit.ng

