Sakamakon Canji: Shugaba Buhari Ya Bayyana Wani Muhimmin Alkawari Da Ya Cikawa 'Yan Najeriya
- Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ta cika alƙawarin kawo canjin da ta yi wa ƴan Najeriya
- Shugaban ƙasar mai barin gado ya bayyana hakan ne a wajen ƙaddamar da wasu gidaje a Abuja
- Shugaba Buhari ya ce aikin ginin gidajen da gwamnatinsa ta yi wata babbar alama ce mai nuna cewa tana tsamo ƴan Najeriya daga ƙangin talauci
Abuja - Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta cika alƙawarin canjin da ta yi wa ƴan Najeriya.
Jaridar Vanguard tace shugaba Buhari, ya bayyana hakan ne ranar Talata lokacin da ya miƙa ƴan makullan sabbin gidajen da hukumar gidaje ta tarayya (FHA) ta gina a Zuba, babban birnin tarayya Abuja, ga mamallakan gidajen.
Shugaban ƙasar a jawabin sa wajen ƙaddamar da rukunin gidajen, wanda ya ke da girman hekta 18.5 ya ƙunshi gidaje 748 cikin rukuni 75, ya buƙace su da su zauna da juna cikin kwanciyar hankali da lumana.
A kalamansa:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Ina miƙa saƙon taya murna ta ga waɗanda suka samu sabbin gidaje a wannan rukunin. Mun cika mu ku alƙawarin canjin da mu ka yi mu ku."
Ya kuma buƙaci mutanen da za su zauna a wajen da su haɗa hannu da hukumar FHA, domin tabbatar da kula da wajen da ba shi cikakken tsaro.
Da ya ke yabawa shugaban hukumar, babban darekta, da jami'an FHA, shugaba Buhari, ya yi nuni da cewa aikin wani manuniya kan ƙoƙarin gwamnatinsa wajen tsamo ƴan Najeriya daga ƙangin talauci, cewar rahoton Tribune.
"Samar da gidaje yana daga cikin ma'aunan gwada talauci da ya addabi mutanen mu, sannan kammala wannan aikin ya samar wa da waɗanda za su amfana mafita." A cewarsa.
"Sabbin waɗanda suka mallaki gidajen kan su, waɗanda suka amfana da wannann shirin, sun samu cigaba sannan sun ƙara matsawa daga ƙangin talauci."
Sanusi Lamido Ya Bayyana Wani Babban Rashin Da Najeriya Ta Yi
A wani rahoton na daban kuma, kun ji yadda tsohon sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi, ya bayyana wata babbar asara da Najeriya ta tafka, a rashin samun mataimakin shugaba Buhari, a matsayin shugaban ƙasa.
Sanusi ya ce Osinbajo ya dace ya hau kujerar shugaban ƙasa, wanda rashin hakan babbar asara ce ga ƙasar nan.
Asali: Legit.ng