Jami’ar Jihar Legas Ta Kawo Hanyar Zirga-Zirga Mai Sauki Ta Keken Scooter, an Kaddamar da Ita

Jami’ar Jihar Legas Ta Kawo Hanyar Zirga-Zirga Mai Sauki Ta Keken Scooter, an Kaddamar da Ita

  • Jami’ar jihar Legas ta kawo hanyar zirga-zirga mai sauki ga dalibai da masu shiga cikin jami’ar da ke Kudancin kasa
  • An kaddamar da kekunan kamfanin TREKK Scooter da za su rage yawan cunkoso da kawo yanayi mai kyau a jami’ar
  • Jami’ar LASU ce ta farko a Najeriya kuma ta gwamnati da ta fara amfani da wannan fasaha mai daukar hankali

Jihar Legas - Jami’ar jihar Legas (LASU) ta sanar da fara aikin keken scooter a matsayin wani yunkurin kawo hanyoyin zirga-zirga a cikin harabar jami’ar da ke Ojo.

Da yake kaddamar da fasahar, daraktan LASU Venture Limited, farfesa Tosin Adu ya ce, an kawo wadannan kekunan ne bisa hadin gwiwar tsakanin kamfanin TREKK Scooters mai samar da kekunan da jami’ar.

Ya kuma bayyana cewa, jami’ar ta yi hakan ne don ba daliban damar zirga-zirga cikin sauki a cikin jami’ar da kuma kiyaye tsaftar cikin jami’ar kanta.

Kara karanta wannan

2023: Makaho ne kadai zai ce Tinubu ya ci zabe, LP ta yiwa APC wankin babban bargo

Yadda aka kawo kekuna a LASU ta Leasg
Kekunan TREKK Scooters da aka kawo a LASU | Hoto: tribuneonlineng.com
Asali: UGC

Hukumar jami’ar Legas ta yi kokari

Ya kuma yaba wa hukumar jami’ar bisa yarda da wannan yarjejeniya da LASU Ventures Limited ta kawo.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar Adu:

“TREKK Scooter za su ba da yanayi mai tsafta a matsayin zabi ga zirga-zriga a harabar jami’ar kuma zai ba dalibai damar bude kekunan da aka ajiye a babban kofar jami’ar, Ojo, Legas, su biya kudi kadan a manhajar TREKK sannan su yi yawo da ita a ko’ina cikin harabar.”

Mr. Isaac Oyedokun, babban jami’in musaya na kafar e-Scooters ya ce, LASU ce jami’ar gwamnati ta farko da ta dauko yi amfani da wannan fasahar.

Wannan fasaha za ta taimaki jami’ar Legas, inji VC

Shugaban jami’ar, farfesa Ibiyemi Olatunjui Bello, mni wanda ya samu wakilcin mataimakinsa farfesa Olufunsho Omobitan ya ce, wannan yunkuri zai taimakawa jami’ar ainun.

Kara karanta wannan

Yaki ake: FG ta fadi dalilin da yasa dauko 'yan Najeriya daga Sudan zai ci $1.2m

Ya kuma bayyana cewa, hakan zai sanya jami’ar ta zama mafi kyau da daraja a nahiyar yammacin Afrika.

Daga nan ya taya jama’a murna tare da kaddamar da kekunan ta hanyar gwada amfani dasu a gaban mambobin ma’aikatan jami’ar.

Fasaha na ci gaba da habaka a duniya, ana yawan kirkiro hanyoyin gudanar da rayuwa ba tare da wata matsala ba a wannan zamanin.

An samu gidan cin abincin da ya kawo mutum-mutumi domin rage yawaitar hannun jama’a a ayyukansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.