Hukumar Jarrabawar JAMB Ta Fitar da Sakamakon UTME Na Wannan Shekarar
- Hukumar jarrabawar JAMB ta cire sakamakon jarrabawar daliban da suka zana jarrabawar a makon jiya
- An kuma bayyana cewa, akwai wadanda ba za su ga sakamakonsu ba saboda matsalar da aka samu a baya
- Hakazalika, JAMB ta bayyana matsayarta ga wadanda basu samu damar rubuta jarrabawar ba kamar yadda aka tsara
FCT, Abuja - Hukumar shirya jarrabawar shiga jami’a ta JAMB ta saki sakamakon jarrabawar UTME na 2023 da aka yi a makon da ya gabata.
A cewar hukumar, dalibai 1,595,779 ne suka zana jarrabawar a cibiyoyi 708 a garuruwa 105 na zagayen kasar nan, The Nation ta ruwaito.
Hukumar ta saki sakamakon tare da bayyana sake sanya ranar da wadanda basu damar rubuta jarrabawar ba za su yi.
A cewarta, dukkan wadanda basu rubuta jarrabawar ba saboda matsalar da aka samu daga JAMB za su sake zaman rubutawa a ranar 6 ga watan Mayu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yadda za a duba sakamakon UTME na bana
Ga duk wanda ke son duba sakamakon jarrabawar, zai iya tura sakon tes: UTMERESULT zuwa 55019 ko kuma 66019.
Za a ga sakamakon ne kadai idan aka yi amfani da lambar wayan da aka yi rajistar UTME da ita a baya.
“Don duba sakamakon, duk wanda ya rubuta jarrabawar na bukatar cikin sauki ya tura UTMERESULT zuwa 55019 ko 66019 ta hanyar amfani da lambar wayan da aka rajista da ita ta haka ne za a ga sakamakon”
Ga wadanda za su sake rubuta jarrabawar, JAMB ta ce:
“Misali, ga wadanda basu halarta ba ko aka sauya musu ranar jarrabawar ko kuma ake bincike kan jarrabawarsu, za su ga: YOU WERE ABSENT, RESCHEDULED OR UNDER INVESTIGATION. Don haka, daliban da ba sa cikin wadancan ne kadai za su ga sakamakonsu.”
Za a saki sakamakon JAMB, amma da matsala
A baya, kunji yadda JAMB tace za ta saki sakamakon jarrabawar bana ta UTME amma kuma akwai matsaloli a kasa game da jarrabawar.
Wannan ya faru ne sakamakon rashin samun dama ga wasu dalibai su rubuta jarrabawar a lokacin da aka tsara.
Don haka, hukumar ta sake ba da wani lokacin a gaba don rubuta jarrabawar ga daidaikun dalibai.
Asali: Legit.ng