Ba Alhakin Gwamnati Ba Ne Samar Da Aikin Yi Ga 'Yan Ƙasa, In Ji Kakakin Buhari, Femi Adesina

Ba Alhakin Gwamnati Ba Ne Samar Da Aikin Yi Ga 'Yan Ƙasa, In Ji Kakakin Buhari, Femi Adesina

  • Ba hurumin Gwamnatin Tarayya bane ta samar wa ko wane ɗan ƙasa aikin yi
  • Alhakin gwamnati shine samar da ingantaccen yanayin da za a riƙa gudanar da kasuwanci
  • Buhari bai yi alƙawarin samar da ayyukan yi miliyan 3 ko wane wata ga 'yan Najeriya ba

Babban mai taimaka wa shugaban ƙasa a fagen watsa labarai Mista Femi Adesina ya bayyana cewa ba hurumin gwamnati bane samar da aikin yi ga duka 'yan ƙasa.

Babban mai taimaka wa shugaban ƙasa a fagen watsa labarai Mista Femi Adesina ya bayyana cewa ba hurumin gwamnati bane samar da aikin yi ga duka 'yan ƙasa.

Femi Adesina
Adesina ya ce aikin gwamnati shine samar da kyayawan yanayi ga kamfanoni da masa'antu don su samar da aiki. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da sashen labaran talabijin na Arise TV a yayin da yake bayyana irin nasarorin da gwamnatin Buhari ta samu a cikin shekaru takwas da ta yi tana mulki.

Kara karanta wannan

Shugaban Hukumar Tsaro a Jihar Arewa Ya Tsallake Rijiya Da Baya a Hannun 'Yan Bindiga, Cikakkun Bayanai Sun Bayyana

Jaridar Punch ta ruwaito Femi Adesina ya na bayyana cewar abinda kawai gwamnati za ta yi shine samar da ingantaccen yanayin da zai ba masana'antu da kamfanoni masu zaman kansu damar yin ayyuka tare da ɗaukar ma'aikata.

Gwamnati bata ɗauki alƙawarin samar da ayyukan yi miliyan 3 ko wane wata ba

Da ya ke amsa tambaya dangane da alƙawarin da shugaba Buhari yayi a zaɓen 2015 na cewar zai riƙa samar da ayyukan yi aƙalla miliyan 3 a kowane wata, sai ya kada baki ya ce ba haka Buharin ya ce ba.

Ya bayyana cewa Buhari ya ƙiyasta adadin yawan marasa aikin yi ne kawai a lokacin, saboda haka ba zai iya tuna ko cewa Buhari ya taɓa faɗar makamanciyar wannan magana ba kamar yadda Vanguard ta wallafa.

Ma'aikatu ne ke samar wa da 'yan ƙasa isassun ayyukan yi ba gwamnati ba

A cewar Adesina:

“Mafiya yawan ayyukan da ake buƙata a ƙasa na zuwa ne daga ma'aikatu masu zaman kan su. Muddun dai akwai ingantaccen yanayi na kasuwanci, ma'aikatu masu zaman kansu za "su cigaba da samar wa 'yan ƙasa ayyukan yi isassu."

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Fadawa Bola Tinubu Alfarmar da Yake Nema a Wajen Gwamnatinsa

Daga ƙarshe, Adesina ya bayyana cewa Shugaba Buhari ya cimma ƙudurori da dama ta ɓangarori daban-daban, irin su ɓangaren mai, gine-gine, harkokin shari'a, da kuma ɓangaren tsaro.

'Yan ta'adda sun kai wa kwamandan yaƙi da daba na jihar Zamfara farmaki

A wani labarin na daban kuma, kwamandan hukumar yaƙi da dabanci ta jihar Zamfara Bello Bakyasuwa ya tsallake rijiya da baya biyo bayan farmaki da 'yan ta'adda suka kai mishi a kan hanyar shi ta zuwa Kaduna daga garin Gusau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng