“Sannu-Sannu Bata Hana Zuwa”: Bidiyon Ma’aurata Da Suke Tare Tun Basu Da Komai Ya Yadu

“Sannu-Sannu Bata Hana Zuwa”: Bidiyon Ma’aurata Da Suke Tare Tun Basu Da Komai Ya Yadu

  • Wasu ma'aurata da suka saki tsoffin hotuna da na sauyawar ban mamaki da suka yi sun yi fice a TikTok
  • A bidiyon da ya yadu, ma'auratan sun fara ne daga rayuwar a lallaba amma suka karbi junansu hannu bibbiyu yayin da suke ta samun daukaka
  • Hoton sauyawarsu wanda ke nuna jin dadi da wadata a tattare da su ya ja hankalin mutane da dama

Wani mutumi ya wallafa yadda suka gina gidansu a matsayin ma'aurata tun basu da komai har zuwa lokacin da Allah ya daukaka su a rayuwa.

Daya daga cikin bidiyoyin da ya saki, ya nuna sun yi aure tun suna da kuruciya sannan suka dunga gwagwarmaya tare har sai da suka samu daukaka a rayuwa.

Mata da miji
“Sannu-Sannu Bata Hana Zuwa”: Bidiyon Ma’aurata Da Suke Tare Tun Basu Da Komai Ya Yadu Hoto: @owolawimalikiyabo
Asali: TikTok

A bidiyon krshe, sun kasance cikin yanayi na farin ciki da kwanciyar hankali bayan shafe tsawon shekaru tare.

Kara karanta wannan

Rundunar Yan Sanda Ta Cika Hannu Da Yan Sara-Suka 98 a Wata Jihar Arewa

Masu amfani da soshiyal midiya da dama da suka ga bidiyon sun gaza yarda da sauyin saboda akwai banbanci sosai daga lokacin da suke gwagwarmaya amma dai da dama sun ce hakan ya basu karfin gwiwar da suke bukata a rayuwarsu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A daidai lokacin kawo wannan rahoton, bidiyon ya samu 'likes' 5000 da martani fiye da 50 a TikTok.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun tofa nasu

@Rennlekej|5 ya yi martani:

"Wow kalli sauyi ya yi matukar kyau."

@user7374433990680 ya ce:

"Walahi sun yi kyau matuka."

@IREAYOMIDE49 ya rubuta:

"Hmmm ya burge ni."

@zahnnybankole:

"Magana ta gaskiya."

@S88000:

"Allah ya kara yi maku albarka. Sannunku da aiki da kula da juna."

@user09o66123494:

"Abun dariya.. Na tayaku murna."

@user1065458174357:

"Ma shaa Allah ina kaunarku."

@user8726198227645:

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan bindiga sun kashe yaran da suka sace a Arewa, sun sako wasu 70

"Gaskiya ne faaaa."

Ku daina amfani da tukwanan 'non-stick' don yana da illa ga jiki, likita ya shawarci jama'a

A wani labarin, wani likita ya gargadi jama'a a kan amfani da tukwanan zamani da ake kira da 'non-stick' saboda yana da sinadaren da ka iya illa ga garkuwar jiki.

A cewar likitan, bai kamata mutane su yi amfani da tukunyar ba da zaran kasan sa ya koke domin yana iya haifar da cutar kansa ko ma ya hana haihuwa. Ya ce abun da ya fi dacewa shine jefar da tukwanan da zaran sun koke.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng