Labari Da Duminsa: Gobara Ta Tashi A Ofishin Hukumar EFCC

Labari Da Duminsa: Gobara Ta Tashi A Ofishin Hukumar EFCC

  • Wani gini a cikin harabar Hukumar Yaki da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa, EFCC, reshen jihar Enugu ya kama da wuta
  • A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Juma'a, 5 ga watan Mayu, Wilson Uwujaren, kakakin EFCC, ya ce matsalar hawa da saukan wutan lantarki ya janyo gobarar
  • Uwujaren ya cigaba da cewa jami'an Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya da na jihar Enugu suka taru suka kashe gobarar

Jihar Enugu - An samu barkewar gobara a ofishin Hukumar Yaki Da Masu Yi Wa Arzikin Kasa Zagon Kasa, EFCC, a safiyar yau Juma'a 5 ga watan Mayu.

An tattaro cewa lamarin, wanda ya faru misalin karfe 12.30 na dare ya shafi daya daga cikin gine-ginen hukumar.

Gobara
Gobara ta lashe wani sashi na ofishin Hukumar EFCC a Enugu. Hoto: Photo credit: Economic and Financial Crimes Commission
Asali: Facebook

Wata majiya daga hukumar ta fada wa jaridar Daily Trust cewa hawa da saukan wutar lantarki ne ya yi sanadin gobarar.

Kara karanta wannan

Onijagbo Na Ijagbo: Gwamnan Kwara Ya Baiwa Shahararren Dan Kasuwar Kaduna Sarauta

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Menene ainihin abin da ya faru?

A cewarsa, jami'an Hukumar Yaki da Gobara na jihar Enugu da Hukumar Yaki da Gobara na Tarayya sun taru sun kashe gobarar.

Mai magana da yawun hukumar, Wilson Uwujaren, shima ya tabbatar da afkuwar lamarin, PM News ta rahoto.

Uwujaren ya yi bayanin cewa ba a rasa rai sakamakon gobarar ba.

EFFC da ICPC sun bukaci a yi watsi da karar Keyamo ta neman a binciki Atiku

A wani rahoton, Hukumar Yaki da Rashawa, ICPC, da Hukumar Yaki da Masu Yi Wa Arzikin Kasa Ta'annati, EFCC, sun yi kira da cewa a yi watsi da karar da Festus Keyamo ya shigar a Babban Kotun Tarayya ta Abuja na neman a binciki tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.

Hukumomin biyu na yaki da rashawa sun ce karar da babban lauyan ya shigar ba ta da inganci don haka a yi watsi da ita nan take.

Kara karanta wannan

‘Dan Baiwa Ya Yi Cin Kaca a Jarrabbawar JAMB, Ya Tashi da 99 Cikin 100 a Lissafi

Karar ta Keyamo ta shafi wani faifan murya da ya bazu a intanet inda aka ji murya da ake ikirarin na Atiku ne na bayani kan hukumomi da suka kafa don karkatar da kudaden gwamnati.

An yi gobara a Kasuwar Balogun

Hakazalika, gobara ta lashe wasu sassan kasuwar Balogun a Lagos Island.

Legit.ng ta rahoto a ranar Talata 28 ga watan Maris cewa sashin da ake sayar da takalmar mata ne abin ya shafa a sananniyar kasuwar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164