An Bada Umurnin Kamo Dan Sandan Da Aka Nadi Bidiyonsa Ya Yi Tatil Da Giya Tare Da Yin Bayan Gida A Wandonsa
- Hukumar ƴan sandan jihar Kwara ta ba da umarnin tsare wani mashayin jam'inta da aka ga ya kwalbe a wani bidiyod
- An sami ɗan sandan ne cikin maye a wani faifan bidiyon da ya yadu a kafar sada zumunta cikin kazanta
- Kwamishinan ƴan sandan jihar yace ɗan sandan na fama da rashin lafiya, wanda yake buƙatar binciken lafiyarsa
A cikin wani faifan bidiyo da ke yadu a kafar sada zumunta a ranar Talata 2 ga watan Mayu, an hango wani mashayin ɗan sanda mai suna Stephen Yohanna yana fitsari a jikinsa.
Gidan talabijin na Channels ta ruwaito cewa, an ga dan sandan yana kashi a jikinsa lokacin da abokan aikinsa suka kamashi a jihar Kwara.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Mohammed Shehu ya tabbatar da faruwar lamarin yayin da yake zantawa da manema labarai a hedkwatar ƴan sanda a Gusau da ke birnin Lokoja.
Da yake jawabi, kwamishinan ƴan sandan jihar Kwara, Paul Odama ya bada umarnin kama mashayin ɗan sandan don bincikarsa.
Sai dai ba a ga fuskar dan sanda na ukun da ke daukar bidiyon ba, inda aka ji daya na cewa, "A'a, lallai Yohanna na bakin aiki".
Kwamishinan ƴan sanda ya fitar da sanarwa game da jami'in
Kwamishinan ƴan sandan, a wata sanarwa yace hukumar ta fusata da ganin wannan bidiyo da ke yawo a kafar sada zumunta, yayin da yace matsalar ta wuce ta shan barasa sai dai a nema masa magani.
Punch ta ruwaito kwamishinan yana cewa:
"Hukumar mu tana sanar da cewa an binciko kuma a gano sifetan da ke ofishin yanki na Share da ke ƙaramar hukumar Ifelodun yanzu haka yana asibiti domin duba lafiyarsa."
Bayan haka, sanarwar tace kwamishinan ya umarci da a sanya ido kan sifetan har zuwa lokacin da za su kammala bincike.
Sojoji sunsake ceto daya daga cikin yan matan Chibok dauke da juna biyu
A wani labarin, Rundunar sojin Najeriya a jihar Borno ta yi nasarar ceto daya daga cikin dalibar makarantar Chibok da `yan ta`addar Boko Haram suka sace.
Jaridar leadership ta ruwaito cewa matar `yar kimanin shekaru 26 mai suna Hauwa Maltha ta kubuta ne daga hannun `yan ta`addan bayan shafe shekaru tara a hannunsu.
Asali: Legit.ng