Gwamna Sanwo-Olu Ya Saki Hotunan Motocin Bas Masu Amfani Da Lantarki Na Farko a Lagas
- Gwamna Babajide Sanwo-Olu zai gwangwaje al'ummar Lagas da wani sabon yunkuri da ya yi a bangaren sufuri a jihar
- Gwamnatin jihar Lagas ta sanar a shafinta na Twitter cewa ta karbi rukunin farko na motocin bas masu amfani da lantarki
- Sabbin motocin bas din suna iya tafiya mai tsawon kilomita 280 idan suka samu cikakken chaji
Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya sanar da isowar rukunin farko na motocin bas masu amfani da lantarki da za su dunga jigilar jama'a a jihar Lagas.
Gwamna Sanwo-Olu ya bayyana cewa ci gaban yana daga cikin kokarin gwamnatinsa na kara zamanantar da kowane bangare na Lagas.
Ya ce sabbin bas din masu amfani da lantarkin za su rage gurbatattun hayaki da kuma karfafa aiki a bangaren sufuri.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya fada ma mazauna Lagas da su tsammaci tsarin sufurin gwamnati mai tsafta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jama'a sun yi martani a kan sabbin motocin bas masu amfani da lantarki a Lagas
Bayan gwamnan ya wallafa labarin a soshiyal midiya, jama'a sun jinjina masa. Sai dai wasu sun soki hakan.
Mgbojikwe Peter Obi Yusuf Datti @cuppydat ya ce:
"Motar bas da zai tsaya a tsakiyar ekoncos ba Nepa da za a yi chajinsa."
Kevin Doge @ogbodo_kevin sya ce:
"Motar da za a dade ana kula da shi baya Najeriya."
Daniel Ayeni @danizydonn ya yi martani:
"Ci gaba mai kyau. Menene cikkken tasarin amfaninsa a wajen jama'a? Ina jira na ga tasirin da bas dinnan da jiragen kasa za su yi wajen al'umma a Lagas."
Matan da aka dauka aikin sharar titi kan albashi N8000 sun magantu
A wani labarin, wasu mata da mazajensu suka mutu wadanda aka dauka aikin sharar titi domin rage masu radadi a jihar Filato sun bayyana irin gwagwarmayar da suke sha a kan albashin N8000.
Matan sun bayyana cewar suna shan wahala saboda har yanzu gwamnati bata yi masu karin albashi ba sannan kuma wasu watannin ma ba a biyansu albashi, ga shi abun da suke samu baya isan su daukar dawainiyar kansu da na iyalin su.
Asali: Legit.ng