“Ki Hau Jirgi Ki Dawo Najeriya”: Martanin Jama’a Bayan Mata Ta Gano Ana Siyar da Tuwo N920 a Landan
- Wata ‘yar Najeriya da ta yi bulaguro zuwa kasar waje ta yi mamakin yadda ta ga ana siyar da tuwo a kan farashi mai ban al’ajabi
- Matar ta yada bidiyon yadda aka fakin tuwo a kwali, inda ake siyar da kowanne dauri daya a kan kudi N920
- Da ake martani ga bidiyon, mutane da yawa sun bayyana ra’ayinsu game da wannan sabuwar kasuwa mai alamar riba
Wata ‘yar Najeriya ya shiga mamaki a kasar waje yadda ta ga an yi fakin tuwon rogo a ana siyarwa kamar wani kayan a zo a gani.
A cewarta, ta yi tafiya ne zuwa Landon, inda ta nemi ta ji nawa ne kudin daurin tuwo, sai aka ce mata ana siyarwa N920.
Ta yada wani bidiyon da ke nuna tuwon a cikin kwali a kafar TikTok, inda ta bayyana kaduwa da lamarin da ta gani mai ban mamaki.

Kara karanta wannan
"Duk Da Na Mallaki Kwalin Digiri Biyayyar Aure Zan Yi" - Matashiya Ta Bayyana a Bidiyo

Asali: TikTok
Jama’ar kafar sada zumunta sun yi taya ta mamaki, sun yi martani mai daukar hankali game da wannan kasuwa mai cike da riba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kalli bidiyon:
Martanin jama’a a TikTok
@senni76:
“Dan kasuwan nan akwai hangen nesa. Wannan shi nake addu’a a kai kullum na samu tunani mai kyau na samun kudi.”
@oxcygin:
“Meye kike tsammani? Ya kamata ki yi tunanin kudin jigila na dan kasuwan.”
@farmersanctus:
“Idan kika ci gaba da latsa kalkuleta kamar haka, kina kwatanta fam da naira kafin ki ci abinci ko siya abu, ba za ki samu damar yin komai ba a landan.”
@larapresh:
“Ki shigo jirgi ki zo ki siya a Najeriya.”
@n.apeter8:
“Ta yaya wannan ya shiga Landan ko dai ana noman rogo a cikin kankara ne.”
@risikot101:
“10 na wannan kenan a Najeriya amma dai na fahimci komai garau.”

Kara karanta wannan
Bidiyon Yadda Mahaukaci Yake Tafiyan Kilomita Da Yawa Zuwa UNIBEN a Kullun, Ya Zauna Yana Rubutu
Yadda amfani da fasahar ChatGPT ya fadar da wata a jarrabawa
A wani labarin, kunji yadda wata ta fadi jarrabawa bayan ta yi amfani da manhajar ChatGPT wajen rubuta jarrabawar a makaranta.
Malamin tuni ya gano tare da bayyana mata cewa ta yi amfani manhajar yanar gizo, don haka ya ba ta makin 0 domin ba aikinta bane.
Jama’ar kafar sada zumunta sun yi martani, sun bayyana yadda ake amfani da irin manhajojin ba tare da an samu matsala ba.
Asali: Legit.ng