Jami'an Yan Sanda Sun Kama Bindigogin AK-47 a Jihar Kano

Jami'an Yan Sanda Sun Kama Bindigogin AK-47 a Jihar Kano

  • Yan sanda sun kama wasu bindigogin AK-47 guda hudu da ake kokarin shigewa da su a jihar Kano
  • Jami'an tsaro da ke sintiri a Kwanar Garko da ke kan hanyar Bauchi zuwa Kano suka gano bindigogin a cikin wata bas kirar Hiace
  • Daya daga cikin mutanen da ke cikin motar ya jefar da buhun bindigogin a lokacin da suka hango yan sandan

Kano - Jami'an rundunar yan sanda a jihar Kano sun kama bindigogin AK-47 guda hudu daga wajen wasu miyagu a hanyar Kano zuwa Bauchi a ranar 25 ga watan Afrilu, PM News ta rahoto.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun jami'in hulda da jama'a na rundunar, SP Abdullahi Haruna-Kiyawa, a ranar Juma'a, 28 ga watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Wata Jihar Arewa, Sun Kashe Yan Farin Hula 15 Da Sojoji 2

Jami'an yan sanda da bindigogi
Jami'an Yan Sanda Sun Kama Bindigogin AK-47 a Jihar Kano Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Yadda aka kama bindigogin AK-47 a Kano

Ya ce wata tawaga da ke fatrol a babban titi ne suka gano bindigogin yayin da suke aikin binciken motoci a Kwanar Garko da ke karamar hukumar Garko ta jihar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kakakin yan sandan ya ce:

"Yayin aiki a hanyar Kano zuwa Bauchi, jami'an yan sandan da ke lura da abubuwa sun hango wata bas din Lite-Hiace da ke kokarin sauya hanya inda daya daga cikin mutanen da ke cikinta ya sauka rike da wani abu da ake shakku kansa.
"Hakan ya ja hankalin tawagar inda hakan ya tilastawa mutumin ajiye kayan tare da tserewa daga wajen."

Ya kara da cewar wani bincike da aka yi cikin buhun ya nuna cewa yana dauke da bindigogin AK-47 guda hudu.

Kiyawa ya ce:

"Tawagar tsaro na hadin gwiwa na nan suna kokarin kama masu laifin da suka tsere."

Kara karanta wannan

Mummunan karshe: Sojoji sun aika 'yan bindiga 5 madakata, sun kwato shanu da makamai

A cewarsa, mukaddashin kwamishinan yan sandan jihar, Mu'azu Mohammed, ya jinjinawa jami'an a kan namijin kokarin da suka yi.

Ya bukaci mazauna jihar da su zamo masu lura da tsaro da kyau sannan su kai rahoton duk wani mutum ko kaya da basu gamsu da su ba zuwa ofishin yan sanda mafi kusa.

Kiyawa ya kara da cewa:

"Suna kuma iya kai rahoto ta lambobin gaggawa na rundunar: 08032419754, 08123821575, 0807609127 da 09029292926."

A wani labari na daban, kwamitin da zai karbi mulki na NNPP a jihar Kano ya zargi gwamnatin Abdullahi Ganduje da yi wa tsarin kafar angulu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng