“Mutuwar Aure 1, Da 1, Yajin Aiki 2”: Matashiya Ta Bayyana Gwagwarmayar Da Ta Sha Kafin Kammala Karatu

“Mutuwar Aure 1, Da 1, Yajin Aiki 2”: Matashiya Ta Bayyana Gwagwarmayar Da Ta Sha Kafin Kammala Karatu

  • Wata matashiya da ta ba da labarin gwagwarmayar da ta sha kafin ta kammala karatun digiri dinta ta yi fice a TikTok
  • Matar ta ba da cikakken bayanin fadi tashin da ta yi ciki harda kula da jinjiri da mutuwar aure
  • Hotonta ya nuna cewa ta kammala karatunta a karshe a bangaren kimiyyar siyasa

Wata matashiya ta bayyana gwagwarfmayar da ta sha kafin ta kammala karatunta na jami'a.

Matashiyar wacce ta mallaki kwalin digiri a yanzu ta bayyana cewa ta yi aure kuma auren ya mutu a lokacin da take makaranta kuma ta kula da danta wanda ya cika shekaru hudu a yanzu.

Matashiya da ta kammala karatu
“Mutuwar Aure 1, Da 1, Yajin Aiki 2”: Matashiya Ta Bayyana Gwagwarmayar Da Ta Sha Kafin Kammala Karatu Hoto: @nana_henna
Asali: TikTok

Ta kuma bayyana cewar a cikin shekaru hudu da ta yi tana digiri, ta fuskanci yajin aiki biyu, annoba daya, cutar damuwa biyu da sauran abubuwa.

Masu amfani da soshiyal midiya da dama da suka yi martani ga labarinta a TikTok sun taya ta murnar kammala karatunta na digiri sannan sun bayyana cewa ita din mace ce mai karfin zuciya.

Kara karanta wannan

Matar Aure Ta Taka Rawa Da Girgiza Yayin da Uwar Mijinta Ta Kai Masu Ziyara, Ta Kawo Masu Abinci Da Yawa

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A daidai lokacin kawo wannan labarin, bidiyon matasgiyar ya tattara 'likes' fiye da 7000 da martani fiye da 400 a TikTok.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@Mahmoudidris ya yi martani:

"Ina ayaki murna. Fatan samun nasara."

@OToblloba ta ce:

"Ya aka yi labarinmu ya yi kama da juna."

@Midecakesnpastries ta ce:

"Mashaa Allah masaniyar kimiyyar siyasa na taya ki murna."

@InorlDebble ta yi martani:

"Lalla ke din mace ce mai karfin zuciya na tayaki murna yar'uwa."

@Trlcla ta yi martani:

"Na tayaki murna yar'uwa."

@splcy36737 ta yi martani:

"Wow na tayaki murna yar uwata mai karfin zuciya."

Matashiya ta rasu jim kadan bayan kammala jarabawa

A wani labarin kuma, mun ji cewa Allah ya yi wa wata dalibar jami'ar jihar Yobe (YSU), Maryam Lawan Goroma, rasuwa jim kadan bayan ta kammala rubuta jarabawarta.

Kara karanta wannan

"Almubazaranci": Budurwa Ta Yi Tafiya Ta Kan Kwai, Ta Fasa Wasu, Bidiyon Ya Yadu

Marigayiya Maryam tayanke jiki ta fadi ne a ranar Alhamis, 27 ga watan Afirilun 2023, sannan aka wuce da ita zuwa asibiti inda aka tabbatar da cewa ta rasu.

Wani abokin karatunta mai suna, Mallam Bukar Maisandari, wanda ya tabbatar da\lamarin ya bayyana cewa, lafiyar Maryam kalau kafin rasuwar ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng