Wata Dalibar Jami'a Ta Fadi Ta Rasu Tana Kammala Jarabawa
- Allah ya yi wa wata ɗalibar jami'ar jihar Yobe (YSU), rasuwa bayan ta kammala rubuta jarabawa
- Marigayiyar mai suna Maryam Lawan Goroma, ta faɗi ne inda jim kaɗan bayan nan aka tabbatar da rasuwar ta
- Tuni aka yi jana'izar ta kamar yadda addinin musulunci ya tanadar a gidan su da ke cikin birnin Damaturu na jihar Yobe
Jihar Yobe - Wata ɗalibar jami'ar jihar Yobe (YSU), Maryam Lawan Goroma, ta riga mu gidan gaskiya jim kaɗan bayan ta kammala rubuta jarabawa.
Jaridar Leadership ta tattaro cewa Maryam ta faɗi ne a ranar Alhamis, 27 ga watan Afirilun 2023, sannan aka wuce da ita zuwa asibiti inda aka tabbatar da cewa ta rasu.
Wani ɗan ajin su mai suna Mallam Bukar Maisandari, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya bayyana cewa, lafiyar Maryam ƙalau kafin rasuwar ta, cewar rahoton Punch.
A kalamansa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Inna Lillaahi Wa Innaa Ilaihir Raji’un. Yanzu cikin baƙin ciki na ke samu labarin rasuwar ƴar ajin mu, Maryam Lawan Goroma."
"Tana cikin ƙoshin lafiya har zuwa yau da rana lokacin da ta faɗi inda jim kaɗan aka tabbatar ta rasu. Allah ubangiji ya yafe mata kurakuran ta. Allah ya sanya Aljannah Firdausi ta zama makoma a gare ta. Ina miƙa ta'aziyya ta ga ƴan'uwa da abokai da dukkanin ƴan ajin mu. Allah ya ba ku haƙurin jure wannan babban rashin. Ameen."
Sai dai, wani Abubakar Zaid, ya bayyana cewa Maryam ta yi ƙorafin cewa tana fama da ciwon ciki lokacin da ake rubuta jarabawar.
An yi jana'izar ta kamar yadda addinin musulunci ya tanadar a yau Juma'a, 28 ga watan Afirilun 2023, a gidan su da ke Sabon Fegi, cikin Damaturu, babban birnin jihar Yobe.
Bayin Allah Da Dama Sun Jikkata, Dukiyoyi Sun Salwanta a Wani Mummunan Fada Da Ya Barke a Jihar Arewa
Jami'ar BUK Ta Yi Babban Tashi, Rijistara Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
A wani rahoton na daban kuma, kun ji cewa Allah ya yi wa rajistaran jami'ar Bayero (BUK), da ke jihar Kano a Arewacin Najeriya.
Malam Jamil Ahmad Salim, wanda ya rasu a ranar Laraba, 26 ga watan Afirilun 2023, ya koma ga mahaliccin sa yana da shekara 60 a duniya.
Asali: Legit.ng