Mutum 14 Sun Mutu, 5 Sun Samu Munanan Raunuka a Wani Hatsarin Jihar Bauchi

Mutum 14 Sun Mutu, 5 Sun Samu Munanan Raunuka a Wani Hatsarin Jihar Bauchi

  • Hatsarin mota a jihar Bauchi ya jawo sanadiyyar mutuwar mutane da yawa, inda aaka ce akalla wasu 14 ne suka rasa rayukansu
  • Hakazalika, an ce wasu mutum biyar sun kwanta dama a hatrsarin da ya faru a hanyar Bauchi zuwa Darazo a jihar
  • Ana yawan samun hadurran mota a Najeriya, lamarin da hukumomi a kasar ke ta’allaka su ga gudun wuce iyaka na direbobi

Akalla mutum 14 ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin motar da ya auku a ranar Alhamis da misalin karfe 12:17 na rana a kauyen Zangoro da ke Bauchi-Darazo a jihar ta Bauchi.

Kwamadan yanki na hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) a jihar Bauchi, Mr Yusuf Abdullahi ne ya bayyana a wani rahoton RTC a jihar Bauchi.

Ya kuma bayyana cewa, akwai wasu mutum biyar da suka samu munanan raunuka a hadarin da a yanzu haka suke jinya, DailyPost ta tattaro.

Kara karanta wannan

Namijin duniya: Lakcara mai mata hudu ya girgiza intanet, hotunansa da, matasa da 'ya'yan sun ba da sha'awa

Yadda hatsari ya kashe mutane a Bauchi
Jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabas a Najeriya | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

A cewarsa, hatsarin ya auku tsakanin wasu motoci biyu; wata Golf 3 Wagon mai lamba AJ 507 GWA da kuma wata Chevrolet.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tattara kayayyakin da suka saura a hatsarin

Kwamandan ya ta’allaka aukuwar hatsarin da gudun wuce kima, inda ya kara da cewa, jami’an FRSC sun tattara komai da ke hanyar tare da gano kudi N73,000, wayoyi guda bakwai, batir din cajin waya daya da kuma jakunkunan hannu guda hudu.

Abdullahi ya ce, gawarwakin wadanda hatsarin ya rutsa dasu yanzu haka suna can a asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi don bincike da gano tushensu.

Ya shawarci masu ababen hawa da su rage gudu, kana su daina saba dokokin hanya da gwamnati ta tsara don tabbatar da tsaron rayukan al’umma.

Ana yawan samun hadurran mota a Najeriya, lamarin yana ci gaba da hallaka mutane da yawa a yankuna daban-daban na kasar, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Yan Bindiga Sun Kutsa Kai Ɗaƙin Taro, Sun Kashe Shugaban Al'umma

An kama matashin da ya kwace wayar wata mata, ya yi kokarin soka mata wuka

A wani labarin, kunji yadda aka kama wani matashin da ya yi kokarin soka wa wata mata wuka a jihar Kano bayan kwace mata waya.

‘Yan sanda sun bayyana yadda lamarin ya faru, da kuma yadda matashin ya amsa laifinsa da kansa bayan kama shi dumu-dumu.

A halin da ake ciki, sace wayar hannu ya zama ruwan dare a jihohin Arewacin Najeriya, musamman Kano da ke Arewa maso Yamma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.