Yan Hisbah Sun Kama Samari da Yan Mata Suna Holewa a Hotel
- Yan Hisbah a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya sun damƙe matasan yara 12 maza da mata a Otal a Birnin Kebbi
- Kwamandan Hisbah na jihar, Ustaz Suleiman Muhammad, ya ce jami'ai sun kama yaran suna aikata laifi a cikin Otal ɗin
- Ya gargaɗi iyaye, samari maza da mata da sauran masu rike da yara su guje wa aikata abinda zai jawo musu nadama
Kebbi - Jami'an rundunar 'yan Hisbah a jihar Kebbi sun kama yara matasa maza da mata 12 suna aikata baɗala a wani Hotel cikin birnin Kebbi, babban birnin jihar, kamar yadda Leadership ta rahoto.
Kwamandan rundunar 'yan sandan Musulunci watau Hisbah na Kebbi, Ustaz Suleiman Muhammad, shi ne ya tabbatar da haka yayin zantawa da yan jarida ranar Alhamis a Birnin Kebbi.
Kwamandan ya ce matasan da aka kama da zargin aikata rashin ɗa'a a Otal ɗin sun kunshi maza Takwas da mata Huɗu kuma dukkansu sun amsa aikata laifin ba tare da gardama ba.
Hisbah ta gargaɗi iyaye da masu Hotel
Rundunar Hisbah ta gargaɗi masu Hotel da su guji baiwa yara maza da mata waɗanda shekarunsu ba su kai ba wurare don aikata alfasha da baɗala.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Bayan haka Hisbah ta ƙara gargaɗi da babbar murya da matasan da ta kama da su guji fita shaƙatawa ba tare da izinin iyayensu ba.
Bugu da kari, rundunar yan sandan Musuluncin ta shawarci iyaye da su kara sanya ido kan 'ya'yansu da waɗanda ke zama a karkashin kulawarsu, su san duk inda zasu je a ko wane lokaci.
Wane mataki Hisbah ta ɗauka kan matasan da ta kama a Otal ɗin?
Ustaz Suleiman Muhammad ya ƙara da cewa tuni suka miƙa yara matasan da suka kama hannun iyayensu bayan sun sa hannu da alƙawarin ba zasu sake aikata laifi makamancin wannan ba.
A wani labarin kuma kun ji cewa Mutum 10 Sun Mutu Yayin da Wata Tanka Ta Fashe a Jihar Filato
Rahotanni sun nuna cewa Tankar, wacce ta ɗauko Man Fetur, ta kucce kana ta yi tunguragutsi kuma ta kama da wuta nan take.
Lamarin ya shafi Motoci da Keke Napep, mutane 10 suka kone ƙurmus, jami'an hukumar yan sanda sun kai ɗauki.
Asali: Legit.ng