Hotunan Ahalin Lakcara Mai Mata Hudu Ya Tada Kura a Kafar Sada Zumunta
- Wani lakcara dan Najeriya ya yada hotunan ahalinsa a lokacin da yake murnar karamar sallah a wannan shekarar
- Mutumin mai mata uku a shekarar da ta gabata ya auri matarsa ta hudu wacce ake kira Hajiya Mamawa inji majiyoyi
- Akalla yana da ‘ya’ya 26 a lokacin da ya yada hoton a kafar Facebook; inda aka maza da mata daga cikin ‘ya’yan nasa sanye da sutura launi daya
Wani dan Najeriya mai aiki a jami’a ya yada hotunan ahalinsa mai yawan gaske a lokacin bikin karamar sallah a bana.
Muhammad Sulaiman, wanda aka fi sani da Baba Lawal, malami ne a Umar Bn Khattab College of Education da ke Tudun Nufawa a jihar Kaduna.
Da aka kirga adadin ‘ya’yansa da ke cikin hoton, sun kai 26, amma a wata tattaunawa da jaridar Punch, ya ce 18 ne kadai nasa.
Baba Lawal ya kara a aure
A hotunan baya-bayan nan da ya yada, Muhammad ya bayyana cewa, ya kara aure, yanzu haka matansa hudu, amma bai hada su a gida daya ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa, sunan matarsa ta hudu Hajiya Mamawa, wacce a kwanakin baya ta rasa mahaifinta, hakan yasa bata cikin hoton.
Sauran matan nasa uku, sun hadu ne domin yin murnar karamar sallah, inda suka godewa Allah bisa ni’imar da ya yi musu.
Hotunan dai a kwanakin nan sun yi yawo matuka a kafar sada zumunta, inda mutane da yawa ke bayyana abin da ke ransu game dasu.
Martanin jama’a
Aliyu Abdul Azeez yace:
“Masha Allah, Allah ya albarkaci ahalin ya kuma kara masa ikon kula da su gaba daya.”
Ajoge Naseer Sanni yace:
“Ina taya ka da ahalinka murnar zagayowar karamar sallah tare. Allah ya ci gaba da karfafa ka ya kuma albarkaci gidanka. Amin.”
Saidu Haruna yace:
“Alhamdulillahi Malam da al’ummarsa Allah ya maka albarka da ahalinka.”
Silver Nyebuchi yace:
"Ina kaunar ahalinka yallabai. Akwai alamar hadin kai kuma akwai kaunar juna. Ina maka addu’ar Allah ya baka abin da za ka kula dasu duka. Allah ya baka a wadace, Amin. Zan iya sanin meye yasa matanka suka rufe fuskokinsu?”
A bangare guda, wasu ahalin kuma fada suke kamar macizai yayin da kudi ya hada su fada a wani yanayin da bai dace ba.
Asali: Legit.ng