Femi Adesina Ya Bayyana Dalilin Kasa Cika Wasu Alkawura Da Buhari Ya Yi

Femi Adesina Ya Bayyana Dalilin Kasa Cika Wasu Alkawura Da Buhari Ya Yi

  • Ta tabbata ashe shugaba Buhari bai san da wasu alƙawura da aka yi wa ƴan Najeriya ba a 2015
  • Femi Adesina ya ce akwai wasu ƴan kanzagi da suka yi ta yin alƙawura waɗanda Buhari bai san da su ba
  • Ya ce ƙungiyoyi da dama masu goyon bayan shugaban ƙasan a 2015 sun riƙa aron bakin sa suna ci masa albasa

Abuja - Hadimin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Femi Adesina, ya bayyana cewa shugaba Buhari baya da masaniya kan wasu alƙawuran da ƙungiyoyin magoya bayan APC suka yi wa ƴan Najeriya a shekarar 2015.

A yayin da ake tunkarar zaɓen 2015, an cika ƴan Najeriya da alƙawura tun daga kan magance tsaro, bunƙasa tattalin arziƙi da samar da ababen more rayuwa da sauran su.

Buhari bai san da wasu alkawuran da aka yiwa yan Najeriya ba
Shugaba Buhari a wajen faretin soji Hoto: @Bashir Ahmad
Asali: Twitter

Sai dai a ranar Alhamis, Adesina ya bayyana cewa, shugaba Buhari bai ma san da wasu daga cikin alƙawuran ba, cewar rahoton Channels tv.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Dalibai 'Yan Najeriya Sun Shiga Tsaka Mai Wuya Kan Hanyar Su Ta Dawowa Daga Sudan

The Cable tace Adesina ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da gidan talbijin na Channels tv a shirin su na 'Sunrise Daily.'

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamansa:

"Abinda ya faru a shekarar 2015 shine akwai tulin takardu da aka yi ta yaɗawa a matsayin manufofin jam'iyya."
"Ba ka sanin wanne ne ya fito daga jam'iyya ƙungiyoyin magoya baya. Misali akwai wata takarda mai taken 'abubuwa 100 da Buhari zai yi cikin kwana 100'. Sai bayan na fara aiki a ƙarƙashin sha na tambaye shi kan wannan takarda, ya ce bai san komai ba dangane da ita."
"Ni ba cikakken ɗan jam'iyya ba ne, don haka ba ni da masaniya idan wasu alkawuran suna cikin manufofin. Amam na san cewa kowace jam'iyya za ta yi alƙawura kafin a zaɓe ta, sannan duk wanda aka zaɓa, dole ne ya mayar da hankali wajen cika waɗannan alƙawuran."

Kara karanta wannan

Bayan Ganawa da Tinubu, Shugaban APC Ya Yi Magana Kan Wanda Za'a Baiwa Shugabancin Majalisa Ta 10

"Abinda na ke cewa shine a shekarar 2015, akwai takardu da yawa waɗanda ko jam'iyya ma ba ta san da su ba, saboda akwai ƙungiyoyin magoya baya da yawa da suka fito da na su alƙawuran."

Gwamnatin Tarayya Ta Sauya Tunani Kan Shirin Cire Tallafin Man Fetur

A wani rahoton na daban kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya, ta sauya shawara kan batun cire tallafin man fetur da ta ke da niyyar yi.

Gwamnatin ta cimma matsayar dakatawa da cire tallafin man fetur ɗin, har zuwa wani lokaci nan gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng