“Wani Irin Mugun Wasa Ne Wannan?” Budurwa Ta Yi Tafiya Kan Kiretan Kwai 4, Bidiyon Ya Yadu
- Wata matashiya ta bi ta kan kiretan kwai a wani bidiyo da ya yadu yayin da wasu mutane biyu suka taimaka mata wajen gangarawa
- Bayan ta yi tafiya kan kiretan kwan a hankali, kafarta daya ya rusa wasu daga cikin kwayayyen a kiret na uku
- Mutane da dama da suka yi martani sun nuna fushinsu cewa ta yi asarar kwayaye masu tsada don kawai ta dauki bidiyo
Wani bidiyo da ya yadu wanda @jking_of_lagos ya wallafa ya nuno lokacin da wata matashiyar budurwa ta yi tafiya a kan kiretan kwai da aka ajiye yayin da take kokarin tsayawa da kyau.
Kafin ta bi ta kan kwan, mutane biyu sun tsaya a gefenta. Daya daga cikinsu na ta bata umurnin da za ta bi.
Matashiya ta yi tafiya a kan kwai
“Dan Allah Ina Sonka”: Budurwa Sanye Da Hijabi Ta Furta Soyayya Ga Saurayi a Bainar Jama’a, Bidiyon Ya Yadu
Matashiyar ta ‘kame na tsawon sakanni sannan ta matsa daga kan kiret din farkon zuwa na biyu. A lokacin da ta isa kan kiret na uku, kafarta daya ya fasa wasu daga cikin kwayayen.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sai dai kuma, ta yi nasarar wucewa kan kiret na daya, biyu da na hudu.
Bayan kallon bidiyon, wasu mutane a sashin sharhin sun yi mamakin dalilin da yasa suka yi asarar kwai da suka yi tsada yanzu don neman suna a TikTok.
Kalli bidiyon a kasa:
Me yasa kuke asarar kwai?
Bidiyon ya samu martani fiye da 100 da ‘likes’ fiye da 3,000 a daidai kawo wannan rahoton.
Ga wasu daga cikin martani a kasa:
Joanna ya ce:
“150 a yankina shine kuke almubazaranci da shi kada ku ji ku yi ta wasa.”
eM mA ya ce:
“Auren Nan Ba Zai Yiwu Ba”: Uba Ya Ba Kowa Mamaki a Wajen Bikin Diyarsa, Ya Fashe Da Kuka Wiwi a Bidiyo
“Kalli irin kwan da kuke batawa abun da zai baku 1M ‘likes’.”
Scott Ferguson ya ce:
“Ku kalla da kyau abun na lotsawa.”
quinitfabrics ya ce:
“Kun tabbata wannan kwan gaske ne.”
Devon ya ce:
“Kwai da ban ci ba na tsawon shekara daya.”
Matashi ya yi tafiya a kan kiret din kwai ba tare da ya fashe ba
A wani labari makamancin wannan, jama'a sun cika da mamaki bayan bayyanar bidiyon wani matashi yana tafiya kan kwai kamar almara ba tare da ya fashe ba.
Asali: Legit.ng