“Ina Kaunarka Dan Allah”: Matashiya Ta Furta Soyayya Ga Saurayi, Ta Roke Shi a Bidiyo
- Ba tare da la’akari da diramar da ya haifar ba, wata matashiya sanye da hijabi ta roki matashi ya so ta a bainar jama’a
- Matashin ya firgita sannan ya umurceta da ta tashi amma ta ki, kuma hakan ya kara ta da mashi da hankali
- Jama’a sun yi martani kan bidiyon da ya yadu inda mutane da dama suka bayyana ra’ayinsu kan dakiyar zuciya irin na yarinyar
Wata matashiyar budurwa sanye da hijabi ta haddasa cece-kuce a bainar jama’a yayin da ta durkusa kan gwiwowinta don furta soyayya ya wani matashi da take kauna.
Da take hada hannayenta waje daya, ta roki saurayin da abun ya duniya ya ishe shi yayin da take furta masa so.
A wani bidiyo da ya yadu a TikTok, matashin ya kirata da sunanta, yana mai umurtanta da ta tashi tsaye. Sai nuna kaduwa yayin da yake kara umurtan budurwar da ta daina abun da take yi amma ta ki.
“Auren Nan Ba Zai Yiwu Ba”: Uba Ya Ba Kowa Mamaki a Wajen Bikin Diyarsa, Ya Fashe Da Kuka Wiwi a Bidiyo
Jama’a sun kewaye su inda wasu suka roki matashin saurayin da ya amsa tayin budurwar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wasu sun yi ikirarin cewa lamarin ya fara ne a jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto amma ba a tabbatar da hakan ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama’a sun yi martani
nwakegocollins ta ce:
“Shin abun da na ji kenan wai baaba farar Yarinya na sonka.”
Young ya ce:
“Saboda musulma ce shiyasa baka so ka aureta.”
Bruno Fernandes ya ce:
“Wannene kuma farar Yarinya na sonka me kike kokarin cewa.”
Aeekay_Mshelia ta ce:
“Lols ya yi kuskure wajen ambatan sunan wata Shamsiyar a tahajud.”
Uba ya fashe da kuka a wajen bikin diyarsa
A wani labarin kuma, wani uba ya tsuma zukatan jama'a da dama a soshiyal midiya bayan ya fashe da kuka harda hawaye a wajen shagalin bikin diyarsa.
“Mai Kama Da Kadangare”: Matashi Ya Koka Bayan Ya Yi Wa Budurwarsa Basaja a Matsayin Wani Daban, Ya Gano Bata Yin Sa
Zuciyar mahaifin amaryar ya karaya yayin da yake bayar da aurenta ga sahibinta kuma nan take ya fashe da kuka wiwi yayin da yake kallon kwayar idanun diyar tasa.
Mutane da dama sun jinjina irin soyayyar da ke tsakanin 'ya'ya mata da iyayensu maza.
Asali: Legit.ng