'Yan Ta'addan ISWAP Sun Yi Awon Gaba Da Jami'an Tsaro Da Ma'aikatan Jinkai a Borno
- Ƴan ta'adda da ake kyautata zaton mayaƙan ƙungiyar (ISWAP) ne sun sace ma'aikatan jinkai a Borno
- Ƴan ta'addan sun lallaɓa cikin dare sannan suka yi awon gaba da ma'aikatan tare da wasu jami'an tsaro
- Ma'aikatan dai suna aiki ne tare da wata ƙungiya mai zaman kanta (NGO) wacce ta ke ayyukan jinƙai a jihar
Jihar Borno - Ƴan ta'addan ƙungiyar Islamic State of the West African Province (ISWAP), sun sace jami'an tsaro biyu da masu aikin jinkai guda uku a jihar Borno.
Masu aikin jinkan ma'aikatan ƙungiyar bayar da jinƙai ce ta Family Health International, FHI 360. Ƙungiya ce mai zaman kanta (NGO) ta ƙasar Amurka.
Channels Tv ta tattaro cewa ma'aikatan guda uku waɗanda duk maza ne, an neme su an rasa ne a gidan da suke zaune a Ngala, wani gari da ke a tsakanin iyaka da tafkin Chadi.
Duk da dai ana zargin cewa ƴan ta'adda ne suka sace su, jami'an tsaron sojoji da ƴan sanda, har yanzu ba su ce komai ba dangane da lamarin, cewar rahoton Punch.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Amma wani majiya ya bayyana cewa wasu jami'an tsaro guda biyu na kamfanin tsaro na Halogen, waɗanda su ke aiki tare da FHI 360, su ma an neme su a rasa a lokaci ɗaya da aka yi awon gaba da ma'aikatan jinƙan.
Majiyar wanda ma'aikacin lafiya ne mai aiki da FHI 360 a Ngala, ya bayyana cewa:
"Ma'aikatan mu ne, mun tashi ranar Laraba ba mu gan su ba. Tare mu ke rayuwa da su a gidan, amma ba mu ji ƙara ko wani sauti da zai sanya mu fahimci wani abu na aukuwa ba.
"Muna zargin cewa ƴan ta'adda ne suka sace su, saboda an taɓa samun irin hakan a watan Afirilun 2022, lokacin da ƴan ta'adda suka sace ma'aikatan MSF, wanda sai daga baya mu ka sani."
'Yan Bindiga Sun Dira Kan Masu Hakar Ma'adanai a Jihar Arewa, Sun Halaka Mutum 6, Da Dama Sun Jikkata
"An san sunayen ma'aikatan jinƙan da aka sace amma ba zan iya faɗin sunan su ba, saboda har yanzu ba a gayawa iyalan su ba."
Yan Bindiga Sun Halaka Masu Hakar Ma'adanai Mutum 6 a Jihar Plateau
A wani rahoton na daban kuma, ƴan bindiga sun halaka wasu mutane masu haƙar ma'adanai a jihar Plateau.
Ƴan bindigan sun dai mamayi mutanen ne suna tsaka da aikin su, a cikin dare sannan suka buɗe mu su wuta.
Asali: Legit.ng