Saudiyya Ta Kwashe ’Yan Najeriya da Yawa Wadanda Suka Makale a Kasar Sudan
- Gwamnatin Najeriya ta bayyana yadda kasar Saudiyya ta bayyana dauko wasu ‘yan Najeriya zuwa birnin Jeddah da ke kasar ta Larabawa
- Ana ci gaba gwabza yaki a kasa Sudan, kasar da ‘yan Najeriya da yawa ke rayuwa da karatu a can tsawon shekaru masu yawa
- Ya zuwa yanzu, gwamnati ta bayyana adadin kudaden da ta ware na daukar hayar motoci bas don dauko wadanda suka makale
FCT, Abuja - Wasu daga cikin ‘yan Najeriyan da suka makale a kasar Sudan sun samu gata daga gwamnatin Saudiyya, inda aka kwashe su daga kasar mai fama da yaki.
A cewar ministan harkokin wajen Najeriya, Zubairu Dada, kasar ta Saudiyya ta tura wasu jiragen ruwa ne suka Sudan domin kwaso ‘yan Najeriyan da suka makale zuwa Jeddah.
Wannan na nufin, za a sake dauko wadannan ‘yan Najeriya daga Jeddah zuwa Najeriya don sada su da ahalinsu da ke jiran isowarsu, Aminiya ta ruwaito.
Wannan na daya daga cikin yunkurin gwamnatin Najeriya da hadin gwiwar kasashe don tabbatar da babu dan Najeriya da ya rage a Sudan cikin sa’o’i 72.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An kashe kudade da yawa wajen kwaso ‘yan Najeriya
A bangare guda, gwamnati ta bayyana cewa, ta kashe akalla N552m wajen yin hayar morocn da za su yi jigilar ‘yan Najeriya daga Sudan zuwa kasar Masar.
A cewar gwamnatin Najeriya, an yi hayar motoci bas guda 40 ne domin kwaso ‘yan kasar daga Khartoum zuwa iyakar kasar Masar a yankin Aswan, daga nan su hau jirgi zuwa Najeriya.
Gwamnatin Najeriya dai na ci gaba da bayyana kokarinta da kuma yadda za ta tabbatar da kwaso ‘ya’yanta daga Sudan ba tare da wata matsala ko tashin hankali ba.
A halin da ake ciki, an ce an tsakaita wuta a yakin da ke gudana a Sudan don ba ‘yan kasar waje damar ficewa.
Yadda ‘yan Najeriya suka makale a Sudan, Saudiyya ta fara tattara ‘yan kasarta
A tun farko, Najeriya ta gaza fara tattara ‘yan kasarta daga Sudan saboda wasu dalilai na tsaro da suka gindiya.
Wannan ya faru sakamakon yadda kasar ta rikice da yaki, inda kowa ke zaman dar-dar a kasar ta nahiyar Afrika.
A halin da ake ciki, kasashe da yawa sun fara tattara mutanensu daga kasar don gudun asarar rayuka da ake gani.
Asali: Legit.ng