'Yan Bindiga Sun Halaka Masu Hakar Ma'adanai Mutum 6 a Jihar Plateau
- Wasu masu haƙar ma'adanai sun gamu da ajalin su bayan ƴan bindiga sun farmake su a jihar Plateau
- Ƴan bindigan sun halaka mutum shida daga a cikin su a mummunan harin da suka kai wajen haƙar ma'adanan
- Harin ya fusata ran mutanen inda matayen su suka fito zanga-zangar nuna adawa da kashe-kashen da ake musu
- ihar Plateau - Ƴan bindiga sun halaka mutum shida a wajen haƙo ma'adanai a ƙaramar hukumar Jos ta Kudu ta jihar Plateau.
Jaridar Tribune ta tattaro cewa, ƴan bindigan suna hakan hanyar su ne ta kai hari a wasu ƙauyuka cikin ƙaramar hukumar lokacin da suka yi kaciɓus da wasu gungun matasa masu haƙar ma'adanai a ƙauyen Farin-Lamba.
Lamarin dai ya auku ne da misalin ƙarfe 9:45 na dare a ranar Litinin.
Wani majiya a kusa da ƙauyen ya bayyana cewa ƴan bindigan waɗanda ake zargin ƴan ta'adda ne, suna arba da matasan suka buɗe mu su wuta inda suka halaka mutum shida daga cikin su nan take, yayin da wasu suka tsira da raunika.
Majiyar ta ci gaba da cewa ƙarar harbin bindigan, ya sanya tsoro a zukatan ƙauyukan da ke makwabta da wajen, inda mutane da dama suka gudu zuwa saman duwatsu yayin da wasu suka shiga daji domin kada a halaka su.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ƴan bindigan kuma sai da suka tafka sata a cikin ƙauyen kafin su wuce, bayan sun kwashe kusan sa'o'i biyu suna cin karen su babu babbaka.
Jaridar Punch tace a ranar Talata, mata daga ƙauyukan sun fito zanga-zanga inda suka ƙulle titin hanyar Farin Lamba-Abuja, domin nuna ɓacin ran su kan kashe-kashen.
Da ƙyar ƴan sanda suka samu motoci suka ci gaba da wucewa ta kan titin bayan sun kwashe sa'o'i suna fama.
Masu Garkuwa Da Mutanen Sun Bi Dare Sun Yi Awon Gaba Da Mutane Da Dama a Abuja
A wani labarin na daban kuma, wasu miyagun masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da wasu bayin Allah, a wani ƙauye cikin ƙaramar hukumar Kwali, ta birnin tarayya Abuja.
Masu garkuwa da mutane sun bi tsakar dare ne yayin da suka aikata wannan aikin ta'addancin.
Asali: Legit.ng