An Mayar Da Sauraron Kararrakin Zaben Jihar Ebonyi Zuwa Birnin Tarayya Abuja
- A wani mataki wanda ya zo da bazata, kotun ɗaukaka ƙara ta umurci da a mayar da sauraron ƙararrakin zaɓen jihar Ebonyi, zuwa Abuja
- Babbar alƙaliyar kotun ita ce ta bayar da wannan umurnin na kotun ta koma zaman ta a birnin tarayya Abuja
- Tuni har kotun ta fitar sanarwar yin biyayya ga wannan umurnin na kotun ɗaukaka ƙarar
Jihar Ebonyi - Babbar alƙaliyar kotun ɗaukaka ƙara, Monica Mensem, ta bayar da umurnin a mayar da sauraron ƙararrakin zaɓen jihar Ebonyi, zuwa birnin tarayya da gaggawa.
Sakataren kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ta jiharz Nyior Sekulla, shine ya sanar da hakan a babban birnin jihar, Abakaliki a ranar Laraba, cewar rahoton Premium Times.
Ya bayyana cewa an ƙulle ofishin kotun sauraron ƙarar wanda ya ke a hedikwatar fannin shari'a na jihar, daga ranar Laraba, domin bin wannan umurnin.
A cewar sa dukkanin wasu ƙararrakin da ke a gaban kotun, za a cigaba da sauraron su a birnin tarayya Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Domin bin umurnin da aka bamu, mu na sanar da masu shigar da ƙara, lauyoyin su da al'umma cewa zaman wannan kotun a Abakaliki ya ƙare daga 26-04-2023; shigar da ƙara, sauraron ƙara da sauran su, daga yanzu za su ci gaba a Abuja."
Da aka tambaye sa ko meyasa aka mayar da zaman kotun zuwa birnin tarayya Abuja, Henry sai ya kada baki ya ce baya da hurumin yin magana akan dalilan, a cewar Daily Post
Sai dai, ya yi nuni da cewa lamarin ya shafi kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ta jihar Rivers da kuwa wata jiha daban.
Har yanzu dai jam'iyyun da abin ya shafa ba su ce komai ba, dangane da mayar da zaman kotun zuwa birnin tarayya Abuja.
Yan Takarar Jam'iyyun ADC Da PDP Sun Maka Gwamnan Gombe a Gaban Kotu
Mun kawo rahoto kan yadda ƴan takarar da suka yi rashin nasara a zaɓen gwamnan jihar Gombe, suka garzaya kotu domin ƙalubalantar nasarar gwamna Inuwa Yahaya.
Ƴan takarar na jam'iyyun PDP da ADC sun ce ba su aminta da sakamakon zaɓen gwamnan jihar ba.
Asali: Legit.ng