Ana Dab Da Fara Kidaya, Gwamnatin Jihar Arewa Ta Yi Kiran a Dakata, Ta Kawo Dalilanta
- Gwamnatin jihar Benue ta sake yin kira da babban murya domin a ɗage ƙidayar bana ta 2023
- Gwamnatin ta yi wannan kiran ne ta hannun hukumar bayar da agaji ta jihar inda tace akwai mutane da dama da ba su a gidajen su
- Gwamnatin ta jihar Benue ta nemi da ka dakatar da ƙidayar bana gabaɗaya har sai ƴan gudun hijira sun koma gidajen su
Jihar Benue - Gwamnatin jihar Benue ta lissafo dalilan ta na ganin cewa bai kamata a gudanar da ƙidayar shekarar 2023 a cikin watan Mayu ba.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar (SEMA), a ranar Talata tace mutane da ƙauyuka da yawa ba za a ƙirga su ba idan aka gudanar da aikin kamar yadda aka tsara.
Ko a makonnin da suka gabata, sai da gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya roƙi gwamnatin tarayya da ta ɗaga ƙidayar har sai ƴan gudun hijira a jihar Benue da sauran jihohin ƙasar nan sun koma gidajen su, cewar rahoton Leadership.
Babban sakataren hukumar SEMA, Dr. Emmanuel Shior, wanda ya ƙara jaddada wannan kiran na a dakatar da ƙidayar, yayin da yake tattaunawa da ƴan jarida birnin Makurdi, ya ce yakamata a ɗage aikin domin kada mutane da dama a kasa ƙirga su.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A kalamansa:
"Mu na kira da a dakatar da ƙidaya a yanzu saboda muna zargin cewa idan gwamnatin tarayya ta ci gaba da shirin, mutane da dama ba za a ƙidaya su saboda ba za a je gidajen su da ƙauyukan su ba."
"Akwai babban ƙalubale dangane da ƙidayar nan da mu ke aiki a kai. Ka da ku manta ƙidaya ba wai ƙirga mutane kawai ake ba, har da gidajen su. Babban ƙalubalen shine an tarwatsa mutane suna cikin sansanin ƴan gudun hijira.
Gogaggen Dan Jarida Peter Enahoro Ya Mutu
A wani labarin na daban kuma, kun ji yadda sanannen ɗan jarida Peter Enahoro ya koma ga mahaliccin sa, bayan yayi shekara 88 a duniya.
Mamacin yana ɗaya daga cikin manyan ƴan jarida da ƙasar nan ke alfahari da su a lokacin rayuwar sa. Ya bayar da gudunmawa sosai a fannin aikin jarida a ƙasar nan.
Asali: Legit.ng