Buhari Zai Bar Najeriya Zuwa Kasar Waje Yayin da Tinubu Ya Dawo Bayan Makonni 5
- Muhammadu Buhari zai halarci taro da Shugaban Ghana ya kira domin kasashen yankin Guinea
- Jawabin da fadar Shugaban kasa ta fitar ya ce jirgin Shugaban na Najeriya zai tashi ne a yau
- A matsayinsa na tsohon Shugaban kungiyar ECOWAS, Mai girma Buhari yana cikin masu jawabi
Abuja - Mai girma Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yana cikin wadanda za su halarci wani taro da za ayi a babban birnin Ghana watau Accra.
A ranar Litinin 24 ga watan Afrilu 2023, sanarwa ta fito daga shafin Facebook cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai bar Najeriya a ranar Talata.
Dalilin barin kasar shi ne zuwa wajen wani taro na musamman na kasashen yankin Guinea, wannan ne karo na uku da za ayi irin wannan zaman.
Mista Femi Adesina ya fitar da sanarwar halartar taron a matsayinsa na Mai taimakawa Shugaban kasa wajen yada labarai da hulda da jama’a.
Jawabin Femi Adesina
"Shugaba Muhammadu Buhari zai bar Abuj zuwa Accra a ranar Talata, 25 ga watan Afrilu, domin halartar babban taron shugabannin kasashe da gwamnatocin hukumar kula da kasashen yankin tekun Guinea (GGC) wanda Shugaban kasar Ghana, Nana Akuffo-Ado ya kira.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
- Femi Adesina
The Nation ta rahoto Femi Adesina yana mai cewa shugaba Buhari yana da ‘yan rakiya zuwa taron.
Masu rakiya zuwa Accra
‘Yan tawagar sun hada da; Ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama, da Mai ba Shugaban Kasa shawara a kan tsaro, Babagana Monguno.
Daraktan Hukumar tattara bayanan sirri na kasa, Ambasada Ahmed Rufai Abubakar yana cikin ‘yan tawagar tare da wasu manyan jami’an gwamnati.
Daily Trust ta ce a cikin wadanda za su yi jawabi a wajen taron akwai Buhari na Najeriya.
Zaman zai kunshi tattaunawa kan yadda za a wanzar da zaman lafiya tare da kawo karshen masu aikata mugayen laifuffuka a yankin kasashen Guinea.
29 Ga Watan Mayu: Fitattun Yan Najeriya 5 Da Ake Ganin Su Buhari Ke Baiwa Hakuri a Sakonsa Na Barka Da Sallah
Tinubu ya ba marada kunya
A ranar Litinin dinnan ne labari ya zo cewa Shugaban ƙasa mai jiran gado, Bola Tinubu, ya duro Najeriya da kwarinsa bayan shafe makonni a turai.
Da yake jawabi ga ɗumbin masoyansa, Tinubu ya share tantama kan zargin cewa jinya ya tafi, har wasu su na yada rade-radin ciwonsa ya yi kamari.
Asali: Legit.ng