Daga Karshe An Bayyyana Ranar Da Bola Tinubu Zai Dawo Najeriya
- Bayan kwashe tsawon makonni baya cikin ƙasar nan, an bayyana ranar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa zai dawo gida Najeriya
- Majiya mai ƙarfi ta kusa da Bola Tinubu ta tabbatar da cewa yau Litinin zai dira a birnin tarayya Abuja
- Bola Tinubu ya yi kwanaki ƙasashen waje inda ya ziyarci ƙasar Faransa kafin nan ya wuce ƙasa mai tsarki domin yin aikin Umrah
Abuja - Majiya mai ƙarfi ta tabbatar da ranar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasan Najeriya Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, zai dawo Najeriya daga hutun da ya tafi.
Jaridar The Cable ta kawo rahoto cewa, Bayo Onanuga, kakakin watsa labarai na kamfen ɗin zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ya ce yau Litinin Bola Tinubu zai dawo ƙasar nan.
Rikicin Sudan: Masha Allah An Samu Kamfanin Jirgin Saman Da Zai Kwaso 'Yan Najeriya Kyauta Bisa Sharadi 1 Rak
A wani rubutu da Onanuga ya yi a shafin sa na Twitter a ranar Litinin da safe, ya ce zaɓaɓɓen shugaban ƙasar zai dira a birnin tarayya Abuja a cikin ranar yau.
A kalamansa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu zai dawo Abuja yau bayan kwashe makonni yana samun hutun da ya cancanta a ƙasar Faransa."
Tafiyar Bola Tinubu ta haifar da cece-kuce
Tinubu ya kwashe makonni baya cikin ƙasar nan, inda da farko ya wuce ƙasar Faransa kafin zuwa ƙasa mai tsarki domin gudanar da aikin Umrah.
Tafiyar sa zuwa wajen ƙasar nan ta sanya an yi ta yaɗa jita-jita da cece-kucw akan lafiyar sa.
A ranar 22 ga watan Maris, hadiminsa na ɓangaren watsa labarai, Tunde Rahman, ya fitar da sanarwa domin bayyana inda zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ya tafi.
Kamfanin Jirgin Sama Na Air Peace Zai Yi Jigilar 'Yan Najeriya Kyauta
A wani rahoton na daban kuma, kun ji cewa babban kamfanin jirgin saman da babu kamar sa a Najeriya ya ce zai kwaso ƴan Najeriya ba tare da ko sisi ba daga ƙasar Sudan.
Kamfanin jirgin saman na Air Peace ya ce zai yi hakan ne domin bayar da irin ta sa gudunmawar domin ganin ƴan Najeriyan da rikicin ƙasar Sudan, ya ritsa da su sun dawo gida cikin ƙoshin lafiya.
Asali: Legit.ng