Allah Sarki Wani Babban Basarake Ya Hadu Da Ajalinsa a Maboyar Masu Garkuwa Da Mutane

Allah Sarki Wani Babban Basarake Ya Hadu Da Ajalinsa a Maboyar Masu Garkuwa Da Mutane

  • Wani babban basarake a jihar Kofi ya gamu da ajalinsa a hannun masu garkuwa da mutane a cikin daji
  • Basaraken ya ce ga garin ku nan bayan ya sha baƙar azaba a hannun miyagun mutanen da suka sace shi
  • Basaraken ya kwanta dama ne kafin a kai ga kai kuɗin fansa har N2m da masu garkuwa da shi suka buƙata a kai musu kafin su sako shi

Jihar Kogi - Barasaken Aghara a ƙaramar hukumar Kabba-Bunu ta jihar Kogi, Cif David Obadofin, ya mutu a hannun miyagun da su kai garkuwa da shi, kwana 12 bayan an sace shi.

Wani majiga daga iyalan basaraken ya bayyana cewa ya mutu ne ranar Alhamis da ta gabata bisa azabtarwar da ya sha a hannun mutanen da suka sace shi, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Wani gini ya ruguje a barikin 'yan sanda, ya kashe, ya danne mutane da yawa

Basaraken Kogi ya mutu a hannun masu garkuwa da mutane
Taswirar jihar Kogi
Asali: UGC

Masu garkuwa da mutanen dai sun amince su karɓi N2m a matsayin kuɗin fanso domin sako shi da wata budurwa mai suna Temidayo Elewa, bayan sun fahimce cewa basaraken ya galabaita sosai.

Wanu majiyar ya kuma ƙara da cewa a yayin da miyagun su ke jiran a kawo kuɗin, sun ƙulle idanun Elewa sannan suka sauya mata wani waje daban cikin dajin domin ɓadda sawu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Pa. Obadofin ya mutu ne kafin a kai ga kai kuɗin fansar ga miyagun da suka sace shi a cikin daji.

A halin da ake ciki, mutanen ƙauyen sun bayyana cewa an sako Elewa wacce aka sace su tare da basaraken, inda yanzu haka tana hannun ƴan'uwan ta tun ranar Asabar.

Wasu masu yin katako ne dai suka yi kaciɓus da ita tana ta gararamba a cikin dajin, inda suka taimaka mata.

Kara karanta wannan

Wani Bawan Allah Ya Mutu A Hanyarsa Ta Dawowa Daga Masallaci A Ranar Sallar Idi

Miyagun sun sake ta bayan sun fahimce cewa mafarauta da ƴan bijilanti da ƴan sakai na Fulani sun kusa ritsa su a cikin dajin.

Air Peace Zai Dawo Da 'Yan Najeriya Kyauta Daga Kasar Sudan

A wani rahoton na daban kuma, kun ji cewa kamfanin jirgin sama na Air Peace ya shirya tsaf domin dawo da ƴan Najeriya da suka maƙale a rikicin ƙasar Sudan.

Kamfanin ya ce zai dawo da su kyauta amma sai gwamnatin tarayya ta cika wani sharaɗi da ya gindaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng