An Samu Kamfanin Jirgin Saman Da Zai Kwaso 'Yan Najeriya Kyauta a Kasar Sudan

An Samu Kamfanin Jirgin Saman Da Zai Kwaso 'Yan Najeriya Kyauta a Kasar Sudan

  • Kamfanin jirgin sama na Air Peace ya nuna shirinsa na kwaso ƴan Najeriya da suma maƙale a ƙasar Sudan
  • Kamfanin ya ce a shirye ya ke ya fara jigilar dawo da su gida domin tseratar da su daga yaƙin da ake a ƙasar
  • Sai dai kamfanin ya kafa sharaɗin cewa sai gwamnatin tarayya ta yi wata huɓɓasa kafin ya iya kwaso su

Abuja - Kamfanin jirgin sama mai zaman kansa na Air Peace, ya bayyana cewa a shirye ya ke ya kwaso ƴan Najeriyan da rikicin ƙasar Sudan ya ritsa da su kyauta.

Kamfanin ya ce zai dawo da su gida kyauta idan gwamnatin tarayya za ta iya kai su wani filin jirgin sama a cikin ƙasashen da ke makwabtaka da ƙasar Sudan, cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Rikicin Sudan: Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Dalilin Da Ya Sanya Ta Kasa Kwaso 'Yan Najeriya

Kamfanin jirgin sama na Air Peace zai kwaso ƴan Najeriya kyauta
Ana ci gaba da fafata rikici a kasar Sudan Hoto: Von.com
Asali: UGC

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban kamfanin Allen Onyema, ya fitar a ranar Litinin.

Shugaban ya yi nuna da cewa ɗalibai ƴan Najeriya da sauran waɗanda rikicin ya ritsa da su a ƙasar "suna buƙatar taimakon mu."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Onyema ya ce dole ne ya taimaka saboda bai kamata Najeriya ta yi asarar ƴan ƙasar ta a wannan ƙasar ba, inda ya ƙara da cewa wannan wani ƙoƙarin sa ne domin tabbatar da cewa ƴan Najeriyan da ke Sudan sun dawo gida cikin ƙoshin lafiya.

Ya bayyana cewa ba komai ba ne za a riƙe hannu a ce sai gwamnati za ta yi ba, musamman a irin yanzu da ake buƙatar ɗaukar mataki cikin gaggawa.

A kalamansa:

"Har ila yau, Air Peace na son kwaso ƴan Najeriyan da suka maƙale a Sudan ba tare da biyan ko sisi ba, idan gwamnati za ta iya kai su wani filin jirgin sama mai tsaro a cikin ƙasashen da ke makwabtaka da Sudan."

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Mahara Sun Halaka Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Kasa da Wasu Manya 4

"Ba komai ba ne za a zura ido sai gwamnati kawai za ta yi ba. Zai zama abin alfahari a gare mu wajen ba kowane ɗan Najeriya da ya maƙale a Sudan jin cewa su ma ƴan ƙasa ne a ƙasar su."
"A shirye mu ke mu yi hakan da gaggawa. Ba tare da ɓata lokaci ba. Duk wani abinda zai ƙara martabar ƙasa, zama ɗaya, haɗin kai da zaman lafiya mu na son hakan. Har ila yau ba ma yin dana sanin yarda da ƙasar mu da ƙaunar ta duk da ƙalubalen da ake fuskanta."
"Idan aka kai su Kenya ko Uganda ko wata ƙasar, za mu je mu ɗauko su. Wasu iyayen har sun fara kiran mu da mu taimaka. A shirye mu ke mu sake yin irin hakan."

Ko a shekarar 2019, Air Peace ya kwaso ƴan Najeriya a lokacin da rikicin South Africa na hare-hare kan baƙar fata ya yi ƙamari.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Aike Da Sakon Murnar Sallah Ga 'Yan Najeriya, Ya Bayyana Wata Babbar Nasara Da Ya Samu

Manyan 'Yan Takarar Gwamnan Jihar Kogi

A wani rahoton kuma, mun kawo manyan ƴan takarar da za su fafata a zaɓen gwamnan jihar Kogi, a ƙarƙashin jam'iyyun siyasa da dama.

Manyan ƴan takarar masu son gadar gwamnan Yahaya Bello na APC sun fito nw daga jam'iyyun PDP, APC da Labour Party.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng