Sojoji Sun Kashe Yan Ta’adda 35, Sun Lalata Sansanoni 2 a Dajin Sambisa

Sojoji Sun Kashe Yan Ta’adda 35, Sun Lalata Sansanoni 2 a Dajin Sambisa

  • Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun yi gagarumin nasara a kan yan ta'addan Boko Haram a yankin Bama da ke jihar Borno
  • Sojoji tare da hadin gwiwar yan bangan CJTF sun murkushe mayakan kungiyar ta'addanci 35 sannan suka lalata sansanoninsu a dajin Sambisa
  • An kuma samo makamai da kayayyaki daga wajen mayakan wadanda suka ji luguden wuta

Borno - Rundunar sojojin Najeriya ta 21 Birgade da ke Bama, Operation Hadin Kai (OPHK) da rundunar bataliya ta musamman tare da hadin gwiwar yan sa kai sun kashe mayakan Boko Haram 35 a wani aikin kakkaba da ke gudana a dajin Sambisa.

Dakarun sojin karkashin jagorancin Birgediya Janar Victor Unachukwu wanda aka fi sani da Emperor, sun kutsa kai mabuyar Boko Haram a kokarinsu na murkushe gaba daya yan ta'addan daga lungu da sako na dajin Sambisa.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Buhari Ya Fadi Lokacin Da Yan Najeriya Da Ke Zaune a Sudan Za Su Fara Dawowa Kasar

Taswirar Najeriya da ke nuna jihar Borno
Sojoji Sun Kashe Yan Ta’adda 35, Sun Lalata Sansanoni 2 a Dajin Sambisa Hoto: The Cable
Asali: UGC

Yadda sojoji suka farmaki yan ta'addan Boko Haram a Bama

Wasu majiyoyi na sirri sun fada ma Zagazola Makama, kwararre kan harkar tsaro a tafkin chadi cewa aikin kakkaban da ya fara daga Awulari a ranar 17 ga watan Afrilu, ya ci gaba har zuwa sauran sansanonin yan ta'addan da ke kewayen Garno da Alafa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya bayyana cewa yan ta'addan sun kuma kai mamaya tare da kakkabe Izzah da Farisu a ranar 19 ga watan Afrilu, inda dakarun suka fafata da yan ta'addan a wani zazzafan arangama.

Sojojin sun sha karfin yan ta'addan bayan sun yi musayar wuta na kimanin mintuna 30, inda suka kashe mayaka 18 sannan suka kwato babura da dama, bindigogin AK 47 da bindigar harbo jirgi.

A cewarsa, daya daga cikin yan sa kai na CJTF ya rasa ransa yayin arangamar.

Kara karanta wannan

Dan Allah a Kawo Mana Agaji, Kasashe Na Ta Kwashe Mutanensu Ban Da Mu", Dalibar Najeriya Da Ta Makale a Sudan Ta Koka

Dakarun sun kuma kutsa zuwa Farisu inda suka kashe karin mayakan ta'addanci 8. A Alafa, an kashe yan ta'adda uku ciki harda wani kwamanda mai suna "Salafi", yayin da aka kwato babura biyu.

A ranar 20 ga watan Afrilu, dakarun sojin kasa sun sake arangama da wasu yan ta'adda inda suka kashe bakwai. Yayin da sauran suka tsere da raunukan bindiga. Dakarun sun gano babbar motar daukar kaya daya da bindigogi biyu.

Dakarun sojin sun ci gaba da kakkabe Garin Glucose inda suka kashe karin mayakan ta'addanci biyu yayin da sauran yan ta'addan suka janye da guje ma haduwa da sojojin.

Bayan ayyukan na musamman da aka shafe kwanaki uku, dakarun sun yi nasarar kakkabe mabuyar yan ta'adda a garuruwan Garno, Alafa, Alafa D, Garin Doctor, Njumia, Izzah, Farisu, Somalia, Ukuba, Garin Glucose, Garin Ba'aba, Bula Abu Amir, a karamar hukumar Bama ta jihar Borbno.

A cikin aikin, an ceto wasu mata da yan ta'addan suka yi garkuwa da su, jaridar The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Wasu Inyamurai Suka Gudanar da Sallar Idi Ya Ja Hankalin Musulman Najeriya

Za a fara kwashe yan Najeriya da ke makale a yakin Sudan Yau ko gobe

A wani labari na daban, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za ta fara kwashe yan Najeriya da ke makale a Sudan a yau Lahadi, 23 ga watan Afrilu ko gobe Litinin, 24 ga watan Afrilu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng