Gwamnatin Tarayya Ta Fara Biyan 40% Na Karin Albashin da Ta Yiwa Ma’aikata Alkawari

Gwamnatin Tarayya Ta Fara Biyan 40% Na Karin Albashin da Ta Yiwa Ma’aikata Alkawari

  • Ma’aikatan gwamnati a Najeriya sun fara ganin karin albashin da Buhari ya yi alkawarin yi musu a wannan shekarar
  • Wannan ya faru ne duba da yadda farashin kayayyaki ya kara tashi a kasar bayan lalacewar tattalin arziki
  • A halin da ake ciki, wasu tuni sun fara karbar kudin, kuma sun shaida lokacin da aka fara biyansu har da bashi

Najeriya - Jaridar Punch ta ce samo daga majiya mai tushe cewa, gwamnatin tarayya ta fara biyan karin 40% na albashi ga ma’aikata a Najeriya.

A tattaunawar da jaridar ta yi da wasu ma’aikatan gwamnati a ranar Asabar 22 Afirilu, 2023, ta ce sun shaida ganin karin kudin a kan albashin da suka karba.

A cewar wasu manyan ma’aikatan da suka nemi a sakaya sunayensu a Ilorin ta jihar Kwara, sun ce sun samu karin ne kan albashinsu na watan Afrilun 2023.

Kara karanta wannan

Binciken ‘Yan Majalisa Ya Jefa Wasu Ministoci a Matsala, An Fito da Zargin $200m

Buhari ya fara biyan karin albashin da ya yi alkawari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Martanin ma’aikatan gwamnati

A cewar wani daga cikin manyan ma’aikatan na gwamnati:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Na karbi kudin da nake bin gwamnati a yau. Haka nan wasu daga cikin abokan aikinmu sun tabbatar da karbar kudin da suke bi. Ya zo a tare da albashinmu na Afrilu."

Haka nan, wani ma’aikacin gwamnati da ya tabbatar da hakan a Ibadan ya ce:

“Tabbas, gaskiya ne. Duk da cewa ni malamin ne a makarantar gwamnatin tarayya, zan iya tabbatar maka na karbi albashin na Afrilun 2023 tare da bashin da nake bi.”

Umar Muhammad, wani malamin jami’ar tarayya a Keffi a jihar Nasarawa ya shaidawa wakilinmu cewa, tabbas ya samu nasa karin, kuma har da bashi an biya shi.

Yadda batun ya faro

Idan baku manta ba, rahotanni a baya sun bayyana cewa, gwamnatin Buhari ta kuduri aniyar karin 40% na albashi ga ma’aikata saboda rage musu radadin cire tallafin man fetur.

Kara karanta wannan

Wani Dan Shekara 37 Ya Wawushe Naira Miliyan 21 Daga Asusun Coci A Legas

Kakakin ma’aikatan kwadago a Najeriya, Olajide Oshundun ya ce, karin zai shafi dukkan ma’aikatan da ke tsakanin mataki na 1 zuwa 17 a kasar.

A tun farko a watan Maris, ministan kwadago Chris Ngigi ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta amince da karin.

Tuni an maka shi a kasafin kudin kasa na 2023

Ya kara da cewa, tuni an sanya batun karin albashin a cikin kasafin kudin 2023, inda yace zai fara aiki daga watan Janairun bana.

A cewarsa, karin an yi shi ne domin rage wa ma’aikata radadin munin tattalin arzikin da ake fama dadashi baya ga hauhawar farashin kayayyaki, sufuri, haya da kudin wutar lantarki.

Ba wannan ne karon farko da gwamnatin Buhari ke amincewa a kara albashi ga wasu ma'aikatan gwamnati ba a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.