“Na Matsu Na Koma Mahaifata Daura”, Inji Shugaba Buhari
- Bikin karamar sallah na yau Juma'a, 21 ga watan Afrilu shine na karshe da shugaba Buhari zai yi a Villa
- Buhari ya ce ya matsu ya mika mulki a ranar 29 ga watan Mayu domin ya tarkata ya koma mahaifarsa a Daura
- Shugaban Najeriyan ya kuma godema mutanen Abuja da suka yi hakuri da shi na tsawon lokacin da ya yi a mulki
Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce yana Allah-Allah ya koma mahaifarsa da ke Daura a jihar Katsina bayan mika mulki a ranar 29 ga watan Mayu, jaridar The Cable ta rahoto.
Buhari ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a yayin bikin sallarsa na tara kuma na karshe a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Na yi sa'a da zama shugaban kasar Najeriya, Buhari
Shugaban kasar ya ce ya yi matukar sa'a da ya jagoranci kasar Najeriya a mataki daban-daban.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma yi godiya ga mutanen Abuja da suka yi hakuri da shi tsawon shekaru bakwai da rabi da suka gabata.
Buhari ya ce:
"Ina godiya ga mazauna Abuja da suka yi hakuri da ni tsawon shekaru bakwai da rabi da suka gabata.
"Na matsu na tafi gida. Da gangan na yi tanadin da zan kasance nesa da ku.
"Na samu abun da nake so kuma baki shiru zan yi ritaya zuwa mahaifata a garin Daura."
Ya ci gaba da cewar:
"Ina kirga kwaaknin. Damokradiyya abu ne mai kyau idan ba don haka ba ta yaya mutum daga daya bangaren zai zama shugaban kasa na wa'adi biyu?"
Yayin da yake kuma jadadda kusancinsa da kasar Nijar, shugaban kasar ya ce:
"Kilomita 8 ne daga mahaifata (Daura) zuwa kasar Nijar."
Wannan ba shine karo na farko da shugaban kasar ke cewa ya matsu ya koma mahaifarsa ba domin a watan Yulin bara, ya bayyana cewa ya matsu ya koma gonarsa, wanda iyaye da kakanninsa suka bar masa a Daura, rahoton Business Day.
Wike ya aika sakon barka da sallah ga Musulmai a jihar Ribas
A wani labarin kuma, mun ji cewa Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya taya daukacin al'ummar Musulmi a jihar Ribas murnar kammala azumin Ramadan cikin nasara da kuma bikin karamar Sallah.
Wike ya kuma yi godiya ga musulmai kan gudunmawar da suka ba gwamnatinsa ta hanyar mara masa baya inda ya yi alkawarin sama masu ingantaccen muhalli inda za su gudanar da ibadah cikin yancin.
A ranar Juma'a, 21 ga watan Afrilu ne daukacin al'ummar Musulmi a kasar suka bi sahun takwarorinsu na duniya wajen gudanar da bikin karamar sallah.
Asali: Legit.ng