Mabiya Addinin Gargajiya Na Son 20 Ga Watan Agusta Ta Zama Ranar Hutu A Najeriya

Mabiya Addinin Gargajiya Na Son 20 Ga Watan Agusta Ta Zama Ranar Hutu A Najeriya

  • Mabiya addinin gargajiya a Najeriya sun koka kan rashin shiga da su sha'anin gwamnati
  • Mabiya addinin gargajiyar sun nemi a ware ranar hutu don bakukuwan addinin su kamar yadda ake wa musulmi da kirista
  • Kakakin kungiyar mabiya addinin gargajiya reshen Jihar Ekiti, ya kuka kan yadda ake neman kuri'ar su amma ake hana su mukamai

Jihar Ekiti - Kungiyar Iseselagba ta Kasa (yan addinin gargajiya) a ranar Litinin sun mika bukatarsu ga Gwamnatin Tarayyar Najeriya don ba wa yan kungiyar hakikinsu a matsayin yan kasa, The Punch ta rahoto.

Kakakin kungiyar (Awise) a Jihar Ekiti, wanda ya ce addinai uku ne a Najeriya - kiristanci- musulunci - da na gargajiya, ya ce an banzatar da yan addinin gargajiya wajen rabon makuman gwamnati.

Shugaba Buhari
Mabiya Addinin Gargajiya Na Son 20 Ga Watan Agusta Ta Zama Ranar Hutu A Najeriya. Hoto: Fadar Shugaban Kasa
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Eid-Ul-Fitri: Gwamna Wike Ya Aika Sako Mai Tsuma Zuciya Ga Yan Najeriya

Lawal, wanda ya wanda ya zanta da manema labarai a Ado Ekiti, babban birnin Jihar Ekiti, ya yi kira ga gwamnati "ta rage mukaman da take ba wa kiristoci da musulmai zuwa ga yan addinin gargajiya."

Muna son ranar hutu kamar yadda addinan musulunci da kirista ke da shi, Lawal

Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta samar da ranar hutu saboda yan addinin gargajiya kamar yadda ta yi ga musulmi da kirista.

A cewarsa:

"Muna kira ga gwamnatin tarayya da jihohi da su ayyana 20 ga watan kowace Agusta a matsayin ranar hutu saboda mu. Ita ce ranar da duk dan addinim gargajiya zai yi addu'a ga gidajensa, su zubar da jini, bukukuwa da neman dacewa a kasar nan. Akwai bukatar ayi hutu saboda mu samu lokacin da zai ishe mu addu'a da morar ranar".

A tuna da masu addinan gargajiya yayin rabon mukamai a Ekiti

Lawal ya yi kira ga gwamnan Ekiti, Biodun Oyebanji, da ya yi duba ga yan addinin gargajiya kamar yadda ya ke ga musulmi da kirista yayin rabon mukamai da zai yi aiki da su tun bayan karbar aiki.

Kara karanta wannan

Barka da Sallah: Atiku Ya Fadi Abin da Yake Damunsa, Tinubu Ya Yi kira ga Musulmi

Ya ce:

"Yayin da mu ke taya murna ga zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu, bisa nasarar lashe zaben da ya gudana a watan Fabarairu, muna kiransa da ya duba cancantar yan addinin gargajiya idan ya karbi mulki.
"Idan an bawa yan addinin gargajiya mukami, za su kara dagewa da yiwa kasa addu'a. Muna ta addu'a ga garuruwa, kananan hukumomi, jihohi da kasa, amma idan muka samu mukami, zamu kara samun kwarin gwiwar addu'a ga kasa.
"Addinai uku ne da mu a Najeriya. Daga karamar hukuma zuwa tarayya, duk lokacin da su ke neman kuri'a, suna nema daga dukkan mu - Kiristoci, Musulmi da mabiya addinin gargajiya. Duk mabiya addinan na yin zabe. Amma mukami, iya musulmi da kirista ne. Ya kamata mu ma a duba mu."

Lauya Mai Addinin Gargajiya Ya Tafi Kotu Da Tufafin Bokaye

A wani rahoton a baya, kun ji cewa Malcolm Omirhobo, wani lauya mai kare hakkin bil adama ya isa kotu a Legas sanye da tufafin masu addinin gargajiya.

Kara karanta wannan

Eid-el-Fitr: Ta tabbata, Sarkin Musulmi ya ce gobe Juma'a ne karamar Sallah a Najeriya

Ya yi wannan shigan ne biyo bayan hukuncin da kotun koli ta yanke na halastawa dalibai saka hijabi a makarantu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164