Karshen Ramadana 2023: Bayanin Ganin Jinjirin Watan Shawwal Na Karamar Sallah a Najeriya
- Ya zuwa yanzu, kwamitin duban wata a Najeriya ya ce ba a wata ba a wasu bangarori daban-daban na Najeriya
- A yau ne al'ummar Musulmi suka kai azumi na 29 a watan Ramadana mai alfarma, inda ake sa ran ganin wata a yau
- Tuni a kasar Saudiyya, an ga watan Ramadana, gobe Juma'a za a yi karamar sallah a kasar ta Larabawa
Najeriya - Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da zuba ido don jin labarin ganin jinjirin watan Shawwal a garuruwa da yankuna daban-daban na Najeriya.
A wata gajeruwar sanarwar da kwamitin duban wata ya fitar da yammacin yau Alhamis, ba a jinjirin watan ba a jihohi sama da biyar na Najeriya.
Sai dai, kwamitin ya ce yana ci gaba da zuba ido da sauraran rahotanni daga sauran jihohi da garuruwa a kasar.
A cewar wani yankin sanarwar:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Ya zuwa yanzu rahotannin da ake samu daga Bauchi, Nafada (jihar Gombe), Maiduguri, Abuja, Dengi (jihar Filato), Odeomu (jihar Osun) duk ba a ga wata ba."
Legit.ng Hausa ta gano cewa, ba a ga wata ba a Najeriya, muna nan muna jiran sanarwa daga ofishin sarkin Musulmi ko akwai labari.
Sarkin Musulmi zai yi bayani
A halin da ake ciki, sarkin Musulmi ya sanar da cewa, a ranar Juma;a ne za a yi sallah karama a Najeriya.
Ya bayyana hakan ne bayan dogon lokacin da Musulman Najeriya suka jira don jin ta bakinsa, kamar yadda wani sako ya nuna.
Wannan na nufin cewa, gobe Juma'a za ta kasance 1 ga watan Shawwal, wanda za ta yi daidai da 21 ga watan Afrilun miladiyyan Annabi Isa.
An ga watan Shawwal a Saudiyya
A wani labarin kuma, kunji yadda rahotanni daga kasar Saudiyya ke bayyanawa da tabbatar da ganin jinjirin watan Shawwal a wannan shekarar.
Hakan na zuwa ne daidai lokacin da Musulmai suka kammala azumi na 29 a cikin watan Ramadana mai alfarma na bana.
A baya, rahotanni daga masana masu bincike kna hasashen yanayi da taurari sun ce ba lallai a ga watan Shawwal a ranar 20 ga watan Afrilu ba saboda wasu dalilai na yanayi.
Asali: Legit.ng