Gobe Sallah Karama: An Ga Jinjirin Watan Shawwal a Kasar Saudiyya
- Hukumomim ƙasar Saudiyya sun sanar da cewa an ga jinjirin watan Shaewal da yammacin Alhamis 29 ga watan Ramadan
- Hukumar kula da manyan Masallatai masu alfarma ta ayyana ranar Jummu'a 21 ga watan Afrilu a matsayin ranar idin ƙaramar Sallah
- Eid al-Fitr, Sallah ce Raka'a biyu da Musulmai ke gudanarwa a karshen Azumi 29 ko 30 na kowace shekara
Kasar Saudiyya ta sanar da cewa an ga jinjirin watan Shawwal, 1444AH yau Alhamis 29 ga watan Ramadan a wurare kamar Tumair da Sudair.
A sanarwan da hukumar da ke kula da Masallatai masu Alfarma guda biyu, Haramai Sharifain, ta fitar, ta ce gobe Jumu'a 21 ga watan Afrilu, 2023 ce ranar Eid al-Fitr (ƙaramar Sallah).
Wannan sanarwa ta ayyana ranar Jumu'a 1 ga watan Shawwal, 1444AH wanda ya yi daidai da 21 ga watan Afrilu, 2023 a matsayin ranar ƙaramar Sallah (Eid al-Fitr).
Jaridar Arab News ta rahoto cewa za'a gudanar da Eid-Al-Fitr a faɗin ƙasar Saudiyya gobe Jummu'a bayan fitowar rana kamar yadda aka saba, kuma tuni shirye-shirye sun yi nisa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sanarwan neman wata tun farko a Saudiyya
Tun da fari, mahukunta a ƙasar Saudiyya sun yi kira ga ɗaukacin Musulmai mazauna ƙasar su fara duban jinjirin watan Shawwal da yammacin Alhamis, 29 ga watan Ramadan, 1444AH wanda ya zo daidai da 20 ga watan Afrilu, 2023.
A wata sanarwa Kotun koli ta bukaci duk wanda Allah ya sa ya ga jinjirin watan da idonsa ko kuma da na'urar zamani ya kai rahoton ga Kotu mafi kusa.
Haka zalika ta sanarwan ta yi fatan cewa duk wanda ya iya ganin jinjirin wata wata ya kai rahoto zai shiga kwamitin duban wata na yankin da yake zaune domin ya ba da gudummuwa kan abin zai amfani Musulmai.
A wani labarin kuma mun Kawo muku jerin wasu muhimman abubuwa game da idin ƙaramar Sallah a Musulunci
A ranar Jummu'a ko Asabar Musulman duniya zasu gudanar da Eid-Al-Fitr bayan kamma azumtar watan Ramadana, na 9 a cikin jerin watannin Musulunci.
Akwai wasu muhimman abubuwa game da wannan idi, wacce take da suna kala daban-daban saboda saɓanin harshe.
Asali: Legit.ng