Muhimman Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game da Karamar Sallah a Musulunci

Muhimman Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game da Karamar Sallah a Musulunci

Idin ƙaramar Sallah (Eid-el-Fitri) wata Ibada ce da mabiya Addinin Musulunci a faɗin duniya ke gudanarwa bayan shafe tsawon wata suna Azumin watan Ramadan.

Watan Ramadan, shi ne wata na Tara a jerin watannin Kalandar addinin musulunci, kamar yadda rahoton jaridar Punch ya tattaro.

A watan Ramadan, Musulmai na kamewa daga ci da sha da kuma abubuwan soyuwar rai kamar saduwa da iyali tun daga fitowar rana zuwa faɗuwarta.

Sallar idi
Muhimman Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game da Karamar Sallah a Musulunci

A wannan wata mai falala da Albarka, Musulmai kan ƙara kusanci da mahaliccim kowa da komai, Allah SWT ta hanyar ƙaraa ƙaimi wajen Ibada da Ambaton Allah.

Haka nan a Watan Ramadan ne aka saukar littafin Allah mai tsarki watau Alkur'ani ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi).

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Hukuncin Addinin Musulunci Idan Bikin Idi Ya Hadu da Sallar Juma'a a Rana Daya

A Najeriya, Musulmai zasu fara shagalin ƙaramar Sallah Gobe Jummu'a idan an ga jinjirin watan Shawwal yau Alhamis.

Idan kuma ba'a ga wata ba, ranar Asabar za'a yi Sallah, musulmai zasu cika Azumi 30 kenan a watannan shekara 1444AH/2023.

Jerin muhimman abubuwa 7

Legit.ng Hausa ta tattaro muku wasu muhimman abubuwa game da idin ƙaramar Sallah.

1. Ƙaramar Sallah ɗaya ce daga cikin sallolin idi da Musulmai ke gudanarwa a kowace shekara, ta biyun ita ce babbar sallah ko ka kirata sallar layya (Eid al-Adha).

2. Musulmai na shagalin ƙaramar Sallah ne saboda ita ce babbar alamar da ke nuna Azumi 29 ko 30 na watan Ramadan ya kare a kowace shekara.

3. Ana yin karamar Sallah watau Eid al-Fitr ranar 1 ga watan Shawwal, wata na 10 a jerin watannin Musulunci, bayan shugabannin Musulmai sun sanar da ganin jinjirin wata.

4. Eid al-Fitr na da sunaye kala daban-daban a yare mabambanta da kuma ƙasashe a faɗin duniya. Ana kiranta da sunan ƙaramar Sallah ko Idi a takaice.

Kara karanta wannan

Asiri Ya Tonu: An Kama Wasu Muggan Mutane Sama da 20 Ɗauke da Makamai Ana Dab da Sallah a Arewa

5. Karamar Sallah, wata sallah ce mai raka'a guda biyu, wacce ake gudanarwa a Fili ko babban wurin taron jama'a.

6. Yin Sallar idi a cikin Jam'i watau cikin Jama'a wajibi ne a Addinin Musulunci kuma ta ƙunshi Kabbara guda Bakwai a Raka'ar farko da kuma guda 5 a Raka'a ta biyu.

7. Bayan kammala Sallah, Musulmai a faɗin duniya na gudanar da shagulgulan murnar hawa idi ta hanyoyi daban-daban, alal misali zama cin abinci.

An ga wata a Saudiyya

A wani labarin kuma Hukumomin Saudiyya sun sanar da cewa an ga jinjirin watan Shawwal yau Alhamis, 29 ga watan Ramadan.

Sun sanar da ranar Jummu'a 21 ga watan Afrilu, 2023 a matsayin ranar hawa idin ƙaramar Sallah ta shekarar musulunci 144AH.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262