Ku Kara Hakuri: Peter Obi Ya Yi Kira Ga Magoya Bayansa da Babbar Murya Kan Makomar Najeriya

Ku Kara Hakuri: Peter Obi Ya Yi Kira Ga Magoya Bayansa da Babbar Murya Kan Makomar Najeriya

  • Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour ya yi kira ga magoya bayansa da su kara hakuri
  • Ya bayyana cewa, an tunzura su lokacin zabe amma suka hakura, don haka yanzu ma su kara hakuri
  • Ya kuma ce ya kamata kowa ya sanya Najeriya a addu’a don ganin ci gaban kasar a nan gaba

Najeriya - Peter Obi, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour, ya bukaci magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu, tare da nuna kamun kai game da tunzura su da ake yi.

A sanarwar da Obi ya fitar a ranar Laraba, ya ce abubuwan da suka faru a Najeriya, ciki har da abin da ya faru a Adamawa a makon nan ya nuna tasirin bin doka da oda.

A cewarsa, a matsayinsa na dan Najeriya mai kishin kasa, ya mai da hankalinsa tare da dukufa ne ga yiwa al’umma hidima da kuma hango gobe mai kyau ga kasar.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Bayan kammala zabe, an sace direban mataimakin gwaman Arewa

Peter Obi ya yi kira ga magoya bayansa
Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na LP | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Najeriya babbar kasa ce, cewar Peter Obi

Ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su dukufa da yiwa kasar addu’o’in nasara da fatan ci gaba mai girma.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A kalamansa:

“Allah ya albarkaci Najeriya kuma a nan gaba babbar kasa ce. Na ikon Allah, girman Najeriya zai bayyana gaba daya, wannan ke nuna yadda ake girmama ta a duniya.
“Duba da wannan, ina kira ga ‘yan Najeriya mutanen kirki da su dukufa da addu’ar ci gaba da girman Najeriya.”

Ku yi hakuri, Obi ga magoya bayansa

A bangare guda, Peter Obi ya yi kira ga magoya bayansa da su yi hakuri tare da nuna kamewa da kankan da kai kamar yadda suka yi a lokacin da aka yi zaben shugaban kasa a Najeriya.

A cewar wani bangare na sanarwar da ya fitar:

Kara karanta wannan

Kaico: Bashi ya yi mata katutu, ta siyar da jaririyarta mai watanni 18 kacal a wata jiha

“An tunzura mu a lokacin zabe, amma muka nuna kamun kai, kishin kasa da kuma hikima saboda muna son gobe mai kyau ga Najeriya ne ba wai hango lalata Najeriya ba.
“Ina kira ga kowane dan Najeriya da ya ci gaba da yin imani da fatan ci gaba ga Najeriya. Muna cikin wannan tafiya tare, kuma shekaru masu kyau na farin ciki suna jiran mu duka a gaba. Allah ya taimaki al’ummar Najeriya da tarayyar Najeriya.”

Peter Obi dai na ci gaba da cewa shine ya lashe zaben shugaban kasa a Najeriya ba Bola Ahmad Tinubu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.