Farfesa Pantami Ya Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Alhaji Aminu Dantata
- Farfesa Pantami ya kai ziyarar ta’aziyya ga Alhaji Aminu Dantata bisa rashin matarsa da ya yi a kwanakin baya
- Pantami ya yi addu’ar Allah ya gafartawa Hajiya Rabi da ta rasu a kasar Saudiyya, aka binne ta a Madina
- A bangare guda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo Najeriya bayan shafe kwanaki takwas yana ibada a Saudiyya
Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani a Najeriya, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya ziyarci daya daga cikin attajiran Najeriya, Alhaji Aminu Dantata.
Pantami ya ziyarci Dantata ne domin yi masa ta’aziyyar rasa matarsa Hajiya Rabi da ya yi a kwanakin baya.
Idan baku manta ba, rahoton da muka kawo muku a baya ya bayyana yadda aka shiga jimami na yadda matar Dantata ta rasu a kasar Saudiyya.
A cewar rahortanni, tuni an yi jana’izar Hajiya rabi a kasa mai tsarki, inda aka binne ta a birnin Madina.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Pantami ya yi addu’ar Allah ya gafartawa hajiya rabi
A ziyarar da Pantami ya kai, ya yada hotunan lokacin da yake gaisuwar ta’aziyyar don jajanta masa bisa wnanan rashin.
Hakazalika, ya bayyana addu’ar Allah ya gafarta mata, ya kuma sanya aljanna ce makomarta.
A cewar sanarwar da Pantami ya yada a kafar sada zumunta ta Twitter:
“Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya ziyarci daya daga cikin dattawan Najeriya masu mutunci, Alhaji Aminu Dantata don yi masa ta’aziyyar rasuwar matarsa, Hajiya Rabi. Ta rasu a kasar Saudiyya kuma an binne ta a Madinah. Allah ya gafarta mata.”
Ba Pantami kadai ba, a ziyarar yana tare da wasu mukarrabansa da kuma masu fada a ji a mulkin Najeriya.
Buhari ya dawo Najeriya bayan aikin Umrah
A wani labarin kuma, kunji yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo daga kasar Saudiyya bayan ziyarar kwanaki takwas na ibada da ziyara a kasa mai tsarki da ke tara Musulman duniya.
A kasar Saudiyya, Buhari ya gana da manyan jiga-jigai da masu fada ‘yan Najeriya da ke zaune a kasar ta Saudiyya don yin buda baki tare dashi.
Ba wannan ne karon farko da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke kai ziyara Saudiyya ba, yana yawan kai ziyarce-ziyarce kasashe daban-daban da ke alaka da Najeriya.
Asali: Legit.ng