An Tara N21m a Coci, Wani Ya Fece da Kudin, Kotu Ta Ba da Belinsa Bayan Gurfanar Dashi

An Tara N21m a Coci, Wani Ya Fece da Kudin, Kotu Ta Ba da Belinsa Bayan Gurfanar Dashi

  • Kotun majistare a jihar Legas ta ba da belin wani mutum mai shekaru 37 da ake zargin ya sace N21m daga cocin Katolika
  • Mutumin mai suna Oyebuchi ya gurfana a gaban kotu ne a lokacin da ‘yan sandan jihar Legas suka maka shi a gaban kuliya
  • Dan sanda mai gabatar da kara ya gurfanar dashi ne da zargin aikata laifuka uku da suka hada da hadin baki, sata da tada hankalin jama’a

Legas, Ojo – Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta gurfanar da wani mutum mai shekaru 37 mai suna Onyebuchi bisa zarginsa da sace kudade mallakin cocin Katolika da suka kai N21m.

Jairdar Punch ta ruwaito cewa, an gurfanar da Onyebuchi ne a ranar Talata 18 ga watan Afrilu bisa zarginsa da aikata laifuka uku; hadin baki, sata da tada hankalin jama’a.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Bayan kammala zabe, an sace direban mataimakin gwaman Arewa

Da yake magana a gaban kotun majistaren, dan sanda mai gabatar da kara sufeto Ayodele Adeosun ya ce, ana zargin mutumin ne da aikata laifin satan a cocin Katolika na Saint Patrick da ke Alaba-Ojo a Legas ranar Laraba 21 ga watan Disamba.

Benjamin Hundeyin
Yadda aka gurfanar da wanda ya saci kudin coci | Hoto: Benjamin Hundeyin
Asali: Twitter

Dalilin tara kudin a coci

Adeosun ya bayyana cewa, an tanadi kudin da Onyebuchi ya sace ne da nufin yin aikin habaka cocin, inda ake zarginsa da karkatar dasu zuwa asusunsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa, laifin wanda ake zargin ya yi daidai da tanadin sashe na 287, 168 da 307 na kudin manyan laifukan jihar Legas.

Bayan da aka gama karanto masa laifuka, Onyebuchi ya takarkare, ya ce sam bai aikata laifukan da ake zarginsa da su ba, Ripples Nigeria ta tattaro.

An ba da belinsa

Da take martani ga bayanan, mai shari’a T.A Popoola a hukuncinta ta ba da belin Onyebuchi bisa sharadin ba da N1m tare da kawo manyan mutum biyu da za su tsaya masa.

Kara karanta wannan

“Ya Siya Gidaje, Motoci, Ya Tura Mutane Umrah”: Mai POS Ya Kashe Miliyan N280 Da Aka Tura Masa Bisa Kuskure

Legit.ng ta tattaro cewa, daya ka’idar da aka sanya masa, dole wanda zai tsaya masa ya gabatar da shaidar biyan haraji ga gwamnatin Legas na tsawon shekaru uku.

Daga nan aka dage ci gaba da sauraran karar har sai ranar Litinin, 5 ga watan Yuni idan Allah ya kaimu.

Sojoji sun sheke dan sanda a kan tabar wiwi

A wani labarin kuma, kunji yadda wasu sojoji suka hallaka wani sanda saboda ya tare motar abokinsa makare da tabar wiwi.

Wannan lamarin ya faru ne a jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya a cikin wannan makon.

Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da bincike don gano tushen rikicin da kuma daukar matakin da ya dace na doka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.