Tashin Hankali Yayin da Mafarauta Suka Bindige Wani Mutum a Zatonsu Zomo Ne a China

Tashin Hankali Yayin da Mafarauta Suka Bindige Wani Mutum a Zatonsu Zomo Ne a China

  • An samu tsaiko a kasar China yayin da wasu mafarauta suka hallaka wani mutum a lokacin da suke farauta a cikin daji
  • Rundunar ‘yan sanda ta kama mutum hudu da ake zargin suna da hannu a lamarin, kuma ana ci gaba da bincike don gano gaskiya
  • Wannan lamarin ya dauki hankali sosai a kafar sada zumunta, mutane da yawa na ci gaba da cece-kuce da ganin sabon lamarin

Kasar China - Wasu mafarauta sun yi wani mutum kallon zomo, inda suka dirke shi da harsashin bindiga, suke sheke shi zuwa kiyama.

Wannan lamarin ya faru ne a kasar China, a lokacin da mutanen ke cikin daji suna yin farautar dabbobi, rahoton BBC News ta ruwaito.

A cewar rahoto, mutumin mai suna Wan g Moujin ya mutu nan take da mafarautan suka harbe shi da bindiga.

Kara karanta wannan

Kaico: Bashi ya yi mata katutu, ta siyar da jaririyarta mai watanni 18 kacal a wata jiha

Mafarauta sun kashe wani mutum a China
Yadda ake farauta a daji | Hoto: widen.net
Asali: UGC

An kuma tattaro cewa, ya zuwa yanzu an kama wasu mutane hudu da ake zargi a kisan mutumin da ya faru a makon jiya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda lamarin ya faru

A kasa kamar China, an ruwaito cewa ba a cika samun yawaitar harbe-harbe da ke kai wa ga mutuwa ba a cikin kasar.

Bayan aukuwar lamarin, ‘yan sanda sun bayyana yadda ya faru, inda suka ce daya daga cikin mutanen hudu ya saki bindiga bayan jin motsi a cikin dajin.

Hakazalika, rundunar ‘yan sandan ta ce, shi kansa wanda aka hallakan ya shiga dajin ne domin yin farauta, China Daily ta ruwaito.

Ganin hakan a matsayin sabon abu, an yi ta cece-kuce da muhawara kan lamarin a shafukan sada zumunta a kasar ta China.

Kasar China na daya daga cikin kasashen Asia masu tsanani kan dokokin zamantakewa da kuma tafiyar da lamurran yau da kullum, musamman ta fuskar dokokin da kasar ke gindayawa.

Kara karanta wannan

Mayakan Boko Haram Sun Kai Kazamin Hari a Jihar Yobe, Sun Murkushe Mutum 9

Dan shekara 6 ya bindige malamar makaranta a Amurka

A wani labarin, kun ji yadda aka bayyana wani labari mai daukar hankali na yadda yaro karami a Amurka ya bindige malamar makarantarsu.

A cewar rahoton Aljazeera, ba a samu dalibi ko daya ba da ya samu rauni ko ya mutu a cikin makarantar mai suna Richneck Elementary School.

Ya zama ruwan dare samun yawaitar harbe-harbe da bindiga a kasar Amurka, musamman a makarantu tsakanin dalibai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.