Ku Fara Duba Jinjirin Watan Shawwal Ranar Alhamis, Sultan Ya Roki Musulmai
- Sarkin Musulmi ya buƙaci daukacin Al'ummar Musulmai a Najeriya su duba jinjirin watan Sallah ranar Alhamis
- Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya nemi a sanar da mahukunta mafi kusa don kawo rahoto ga kwamitin duban wata
- Ya kuma ƙara tunawa Musulmai muhimmancin fitar Zakkatul Fitr a kan lokaci domin wajibi ce ga masu rufin asiri
Sokoto - Mai Alfarma Sarkin musulmi kuma shugaban majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA) ya fitar da sabuwar sanarwa yayin da watan Azumi ya zo ƙarshe.
Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya roƙi ɗaukacin al'ummar Musulmai a lungu da saƙon kasar nan su duba jinjirin watan Shawwal ranar Alhamis, 29 ga watan Ramadan, 1444AH.
Daraktan gudanarwa na majalisar kolin harkokin Addinin Musulunci a Najeriya, Arc. Zubairu Haruna Usman-Ugwu, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.
Daily Trust ta rahoto sanarwan na cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Bayan shawarin da kwamitin duban wata ya bayar, Sarkin Musulmi kuma shugaban NSCIA ya roki Musulmai su duba jinjirin watan Shawwal bayan faɗuwar rana a ranar 29 Ramadan, 1444AH daidai da 20 ga Afrilu, 2023."
"Idan Musulmai suka ga jinjirin watan kuma ya cika sharudɗan kwamitin duban wata, daga nana Mai Marataba Sarkin Musulmi zai sanar da Jumu'a 21 ga watan Afrilu a matsayin 1 ga watan Shawwal, 1444AH kuma ranar Idul Fitr."
"Haka nan idan jinjirin watan ya ɓuya ba'a gan shi ba a wannan rana, ranar Asabar 22 ga watan Afrilu, 2023 zata zama ranar ƙaramar Sallah."
Daga ƙarshe ya roƙi al'ummar Musulmai, bayan hanyoyin sanar da ganin wata da aka saba a kowane yanki, zasu iya tuntubar mambobin NMSC domin kai rahoton ganin jinjirin watan Shawwal.
Sultan ya tunatar da Musulmai kan Zakkar fidda kai
Bugu da ƙari, Sultan ya bukaci mabiya addinin musulunci su tuna cewa Zakkatul Fitr wajibi ce ga duk mai ƙarfi ya baiwa marasa ƙarfi a yankinsa.
Saboda haka ya ƙara kira ga duk wanda Zakkar ta hau kansa bayan tabbatar da ya cire Zakkar kuma ya tabbata ya fitar kuma ya baiwa mutanen da suka dace a kan lokaci.
A wani labarin kuma A Watan Ramadan, Wani Mutumi Ya Kutsa Kai, Ya Caka Wa Liman Wuka Ana Tskaa da Sallar Asuba
Wani mutumi da shammaci mutane, ya kutsa har zuwa wurin Liman ya daɓa masa wuƙa sau biyu yayin da aka tafi Sujjada.
Asali: Legit.ng