Kotu Ta Kwace Rawanin Sarki Mai Martaba a Jihar Ondo Kan Abu 1

Kotu Ta Kwace Rawanin Sarki Mai Martaba a Jihar Ondo Kan Abu 1

  • Babbar Kotun jiha ta warware rawanin wani Sarkin gargajiya mai martaba a jihar Ondo saboda saɓa wa tsari wajen naɗa shi
  • Masu shigar da ƙara sun shaida wa Alkalin Kotun cewa Sarkin ba ɗan gidan da ya kamata su samar da magajin Sarki ba ne amma gwamnati ta naɗa shi
  • Da yake yanke hukunci, Alkalin Kotun ya haramtawa Basaraken ayyana kansa a matsayin Sarki daga yanzu

Ondo - An kwance rawanin Sarkin gargajiya mai daraja a matakin farko, Oluoke na masarautar Oke-Igbo da ke karamar hukumar Ile-Oluji/Oke-Igbo, jihar Ondo, Oba Babajide Lawrence Oluwole.

Babbar Kotun jiha mai zama a birnin Ondo ta soke naɗin Basaraken bayan ta gamsu cewa ba ɗan gidan Sarautar da ya dace su karbi mulki bane.

Oba Babajide Lawrence Oluwole.
Kotu Ta Kwace Rawanin Sarki Mai Martaba a Jihar Ondo Kan Abu 1 Hoto: channelstv
Asali: UGC

Channels tv ta rahoto cewa gidan Sarautar Kugbaigbe ne ya kamata su samar da sabon Sarki, wanda zai karbi sanda mafi daraja a garin.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC Ta Doke Manyan Abokan Karawarta, Ta Lashe Ƙarin Kujerun Yan Majalisa 8

Yarima guda biyu daga gidan sarautar Aare Kugbaigbe, Rufus Adekanye da Temitope Adeoye, shugaba da Sakataren gidan sarautar ne suka kalubalanci matakin gwamnatin jiha na naɗa Basaraken a gaban Kotu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ta bakin lauyansu, Olusola Ebiseni, masu shigar da ƙara sun faɗa wa Kotu cewa wanda suka kawo ƙara ba ɗan gidan Sarautar Aare Kugbaigbe ba ne, kuma gidan ne ya kamata ya samar da sabon sarki.

Wane hukunci Ƙotu ta yanke?

Da yake bayyana hukuncin da Kotu ta yanke, mai shari'a Ademola Enikuemehin, ya aminta cewa Oluwole ba ɗan gidan da ya dace su samar da mai martaba Sarki bane.

Bisa haka Alkalin ya ce Oluwole bai cancanci hawa karagar mulki ɓa idan aka yi la'akari cewa bai fito daga gidan magadan Sarautar ba.

Daga nan kuma Kotu ta umarci wanda ake ƙara da ya dakatar da nuna kansa a matsayin Sarkin Olu-Oke na Oke-Igbo a jihar Ondo, rahoton Tribune ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Dawo-dawo: PDP ta sake samu kujerar majalisa wakilai ta tarayya a jihar Sokoto

A wani labarin kuma Bayan Gama Zabe Tas, An Fallasa Yadda Atiku, Peter Obi da Kwankwaso Suka Yi Wa Tinubu Aiki a 2023

Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, ya ce rabuwar kawunan Atiku Abubakar, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso ne ya taimaka wa Tinubu wajen cin zaɓe a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262