Ba Lallai a Ga Watan Shawwal a Ranar Alhamis Mai Zuwa Ba, Inji Cibiyar Binciken Sararin Samaniya
- Wata sanarwa daga masani yanayi da sararin samaniya ta ce, ba za a ga wata ba a ranar Alhamis din nan da ke tafe
- Musulmai a duniya na ci gaba da azumin watan Ramadana, inda suke tsammanin karewar watan a ranar Alhamis ko Juma’a
- A wata kasar Musulmai, an hana limamai rike wayoyin hannu a lokacin da suke jan sallar Tarawiy ko Tahajjud
Dubai, daukar Larabawa - Cibiyar nasarin taurari a sararin samaniya ta duniya (IAC) ta ce, babu alamar ganin jinjirin watan Shawwal a ranar Alhamis, 29 ga watan Ramadan, wanda ya yi daidai da 20 ga watan Afrilu.
Saboda haka, cibiyar ta ce, akwai yiwuwar a yi azumi a ranar Juma’a, inda za a tashi da Idin karamar sallah a ranar Asabar 22 ga watan Afrilu, Saudi Gazette ta tattaro.
Dan Takarar Majalisa Na Jam'iyyar Labour Ya Dauki Hayar Makasa Sun Kashe Abokin Hamayarsa Na PDP A Ebonyi
Wannan na fitowa ne daga wata sanarwar da cibiyar ta fitar a shafinta na Twitter, inda tace ta duba hakan ne a hasashenta na gano ranar karamar sallah na bana.
Sai dai, ta ce hukumomin da suka dace kuma suke aiki kan ganin wata ne za su tabbatar da hakan daidai da ganin watan ko akasin haka.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ba za a ga wata ba ranar Alhamis
Ganin watan a ranar Alhamis zai ba da wahala, domin yana bukatar amfani da madubin duba-rudu, kamar yadda wani masanin yanayi ya bayyana a cikin sanarwar.
A cewarsa:
“Ba zai yiwu a ga wata a ranar Alhamis mai zuwa ba da ido daga kowanne yankin Larabawa da duniyar Musulmai.
“Watan ba zai ganu da madubin duba-rudu ba a ranar Alhamis a yawan kasashen Larabawa, sai dai ga yankunan Yammacin Afrika kama daga Libya, don haka ranar Asabar ce za ta zama ranar farko da Idin karamar sallah.”
Wasu kasashe za su yi sallah ranar Juma’a
Masanin ya bayyana cewa, dalilin hakan kuwa ba komai bane face yadda yanayi zai kasance a yankin, inda yace zai shafi ganin watan ko da kuwa an yi amfani da mabudin duba-rudu ne, Zawya ta tattaro.
Hakazalika, sanarwar ta IAC ta ce, masanin ya ce tabbas wasu kasashen Musulmai za su ga watan ta hanyar amfani da madubin duba-rudu, don haka wasu za su yi sallah a ranar Juma’a.
Musulmai a duniya kan azumci watan Ramadana a kowacce shekara, sukan yi azumin kwanaki 29 ko kuma 30 a watan.
A kasar Kuwait kuwa, kunji yadda aka hana limamai amfani da wayoyin hannu wajen karatun sallah a lokacin Tarawiy da Tahajjud.
Asali: Legit.ng