Na Yafe Wa Kanawa Nima Ina Roko A Yafe Min, Gwamna Ganduje

Na Yafe Wa Kanawa Nima Ina Roko A Yafe Min, Gwamna Ganduje

  • Cikin sakon bankwana da Ganduje ya fitar, gwamnan ya roki yafiyar al'ummar Kano
  • Ganduje ya ce a shekarun da ya shafe a gwamnati, dole akwai guraren da ya yi kuskure, kuma ya na rokon yafiya
  • Da yawan mutane na tofa albarkacin bakin su, wasu sun yafe, wasu sun shimfida sharadi kafin su yafe, wasu na cewa basu yafe ba

Jihar Kano - Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya roki yafiyar mutanen Jihar Kano, Daily Trust ta rahoto.

Gwamnan, yayin da halarci Ramadan Tafseer a masallacin Juma'a na Al-Furqan, Alu Avenue Kano, ya ce kwanaki kadan suka rage masa a ofis, saboda haka akwai bukatar ya nemi yafiya.

Gwamna Ganduje
Ganduje ya nemi yafiyar Kanawa. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Na yafe wa duk wanda ya bata min, Ganduje

Ya ce a nasa bangaren, ya yafe wa duk wanda ya bata masa kuma ya na rokon yafiyar kowa.

Kara karanta wannan

Muhimman Abubuwa 7 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Malamin Makarantar Da Ya Lashe Zaben Gwamnan Kebbi

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Da wannan, wa'adi a matsayin gwamnan Kano ya zo karshe. Ina muku bankwana da fatan alheri.
"Ga wanda na batawa, dama malam ya gaya mana muhimmancin yafiya. Ni a bangare na, na yafewa kowa. Duk abin da wani ya fada a kaina na yafe masa. Nima ina rokon yafiyarku. Nagode," in ji Ganduje.

A wani Tafsirin, da Sheikh Nasidi Abubakar Goron Dutse ya jagoranta, Ganduje ya ce:

"Na shafe shekara shida a matsayin kwamishina, shekara takwas mataimakin gwamna yanzu kuma na yi shekara takwas a matsayin gwamnan Jihar Kano. Dole in godewa Allah kan wannan ni'imomin.
"Amma tsawon wannan lokaci, dole akwai wuraren da na yi dai-dai da ba dai-dai ba. Wani lokacin wani zai yi laifi a dauka kai ne. Duk abin da na yi ba dai-dai ba, dan Allah ku yafe min," ya roka.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Dan takarar APC a Sokoto ya lallasa mataimakin gwamna, ya lashe kujerar sanata

Martanin wasu al'umma game da neman yafiya na Ganduje

Sai dai, biyu bayan bayyanar tagwayen bidiyon a kafafen sada zumunta, akwai dubannin martani daga mutane a ciki da wajen Jihar Kano.

Yayin da wasu ke cewa sun yafe masa, wasu na yabawa gwamnan kan neman yafiyar da ya yi.

A daya bangaren, wasu sun sanya sharadi kafin su karbi rokonsa, yayin da wasu ke cewa ba za su yafe masa ba.

Wani Mas'ud Abdulhamid ya ce:

"Mun yafe maka mai girma gwamna, Allah ya yafe mana gaba daya."

Reedwan Shagari cewa ya yi:

"Mutanen Kano zasu yi kewar gwamna mutumin kirki. Ganduje na da kirki duk da kiyayyar da ake nuna masa, amma bai damu ba."

Yakuba Magaji Mani ya ce:

"Ina malamin mu, Abduljabbar? Ka sake shi idan kana so mu yafe maka."

Mustapha Idris Abdullahi:

"Mun yafe maka Baba. Allah ya kara ma lafiya"

Mubarak Sani Lambu ya ce:

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Allah Ya Yi Wa Shahararren Sarki A Arewa Rasuwa Yana Da Shekara 76

"Dan Allah mutanen Kano mu yafe komai ya wuce. Mu yafe wa Baba Ganduje."

Ganduje Ya Magantu Kan Dalilan Canja Kudi

A wani rahoton, gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya zargi Godwin Emefiele gwamnan babban bankin kasa CBN ta bijiro da canja kudi saboda rashin samun tikitin takara.

Gandujen ya ce zafin rashin samun tikitin takarar shugaban kasa ya sa Emefiele bai so a yi zabe ba ya bullo da batun canjin kudin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164