‘A Zauna Lafiya’: Fintiri Ya Fito Ya Yi Bayani Bayan Barkewar Rikicin Siyasa a Adamawa
- Gwamnan jihar Adamawa ya kira ga a zauna lafiya a jiharsa bayan kammala cikon zaben gwamna
- Ya ce ya kamata shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saka baki a rikicin siyasan da ke faruwa a jiharsa
- An ayyana Aisha Binani a matsayin wacce ta lashe zaben gwamnan jihar Adamawa da ke Arewa maso Gabas
Jihar Adamawa - Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa ya ba da shawarin kowa ya zauna lafiya kuma a kwantar da hankali bisa abin da ke faruwa a jiharsa bayan zabe.
An samu tashin-tashin a Adamawa bayan da baturen zabe a jihar, Hudu Yunusa Ari ya sanar da sakamakon zaben gwamna, inda yace Aisha Binani ta APC ce ta lashe zaben.
A cewar gwamnan, tun farkon fara zabe a jihar Ari ke kokarin kai hakurin mazauna jihar bango, Daily Trust ta ruwaito.
Ya kamata Buhari ta tsoma baki, inji Fintiri
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidan gwamnatin jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya shiga lamarin, inda yace bai kamata shugaban ya yi biris da lamari irin wannan ba.
A kalamansa:
“Muna kira gare shi da ya yi bayani, muna kira gare shi d aya dauki mataki. Na yi imani cewa ba zai dauki jam’iyya ba a wannan lamarin.”
Baturen zabe na INEC ya ayyana Aisha Binani a matsayin zababbiyar gwamnan Adamawa
A tun farko, baturen zaben ya bayyana cewa, Aisha Binani ce ta lashe zaben jihar Adamawa, duk da kuwa a sanarwar da muka gani bai fadi yawan kuri’u ba, TheCable ta ruwaito.
Sai dai, Mele Lamido, jami’in zaben INEC a zaben gwamnan jihar ne ke da hurumin sanar da sakamakon zaben daidai da ka’idar INEC.
Saboda haka, hukumar zabe ta INEC ta bayyana dakatar da tattara sakamakon zaben jihar, tare da gayyato baturen zaben da ya gaggauta zuwa hedkwatarta a Abuja.
Ya zuwa yanzu, ba a san me zai biyo baya ba, kuma hukumar zabe ta INEC bata bayyana yaushe za a ci gaba da tattara sakamakon zaben na Adamawa ba.
Wannan ne karo na biyu da ake dage tattara sakamakon zaben jihar da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.
Asali: Legit.ng