Allah Ya Yi Wa Shahararren Sarki A Arewa Rasuwa Yana Da Shekara 76

Allah Ya Yi Wa Shahararren Sarki A Arewa Rasuwa Yana Da Shekara 76

  • Mutanen yankin Abuja Municipal a babban birnin tarayya sun shiga zaman makoki biyo bayan rasuwar babban sarkin yankinsu
  • Hakan na zuwa ne yayin da Sa'akaruyi na kasar Karu, Cif Emmanuel Kyauta Yepwi, ya rasu yana da shekaru 76, wani daga iyalan ya tabbatar
  • Majiyar daga iyalan ya kuma ce an kwantar da marigayi Sa'akaruyi a wani asibiti a Kano kafin ya rasu, yana mai cewa za a dawo da gawarsa zuwa FCT Abuja

FCT, Abuja - Sa'akaruyi na masarautar Karu a Abuja Municipal (AMAC), Cif Emmanuel Kyauta Yepwi, ya rasu yana da shekara 76 a duniya.

Wani dangin margayin sarkin, Habaku Samson, wanda ya tabbatar wa jaridar Daily Trust afkuwar lamarin, a ranar 15 ga watan Afrilu, ya ce ya rasu ne bayan gajeruwar rashin lafiya a ranar Asabar a wani asibiti mai zaman kansa a Jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Muhimman Abubuwa 7 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Malamin Makarantar Da Ya Lashe Zaben Gwamnan Kebbi

Marigayi.
Cif Emmanuel Kyauta Yepwi, ya rasu yana da shekaru 76. Hoto: Chief Emmanuel Kyauta Yepwi
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wani na kusa da iyalan marigayin ya yi karin bayani

Ya ce an kwantar da marigayi Sa'akaruyi a wani asibiti mai zaman kansa a jihar Kano kafin ya rasu, ya kara da cewa za a kawo gawarsa birnin tarayya Abuja.

"Misalin karfe 12 na rana a yau, an kira waya daga Kano cewa Sa'akaruyi na Karu ya rasu a asibiti. Za a dawo da gawarsa zuwa Abuja ta jirgin sama," in ji shi.

Mr Samuel Danjuma, mataimaki na musamman ga Sanata Philip Aduda, wanda aka ce dan wa da kani ne da marigayin basaraken, shima ya tabbatar da rasuwarsa.

Babban rashi a kasa yayin da tsohon minista daga kudu maso yamma ya rasu

A wani rahoton a baya, Legit.ng ta rahoto cewa tsohon karamin ministan makamashi da karafa, Cif Oyekunle Oluwasanmi ya riga mu gidan gaskiya.

Kara karanta wannan

Jerin Matan Arewa Da Suka Ciri Tuta A Siyasar Najeriya Da Maza Suka Yi Kaka-Gida

Oluwasanmi ya rasu ne a ranar Alhamis, 21 ga watan Yulin 2023. Sanarwar rasuwarsa ta fito ne cikin wata takarda da iyalansa suka fitar.

Marigayin ministan dan asalin garin Ipetu Ijesha ne a karamar hukumar Oriade na jihar Osun, inda ya kasance mai kwazo wurin aikin gina al'umma har zuwa karshen rayuwarsa.

An nada shi a matsayin karamin ministan makamashi da karafa ne a shekarar 1997.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164