Tarihi Ya Fara Manta Elon Musk Yayin da Arzikin Bernard Arnault Ya Haura Zuwa $210bn
- Attajiri dan kasar Faransa, Bernard Arnault ya ga yadda dukiyarsa ta tashi zuwa sama da $200bn a rana daya, inda ya bar Elon Musk a baya
- Karin kudin Arnault na zuwa ne a daidai lokacin da kamfaninsa na kayan karau, LVMH ya samu cinikin kusan $12bn nan take
- A bangare guda, a nan gida Najeriya, Aliko Dangote ya samu karuwar sama da $538m a rana guda daga kasuwancinsa
Attajirin da ya fi kowa kudi a duniya, Bernard Arnault na ci gaba da yiwa Elon Musk fintinkau a cikin wannan shekarar.
A cewar rahoton Bloomberg, attajirin dan kasar Faransa ya yi cinikin kayayyakinsa na karau, inda Tesla, kamfanin Elon Musk ke ja da baya.
Arnault ya kafa tarihi a fannin karin dukiya
Bloomberg ta ce, Arnault ya samu karin $12bn a dukiyarsa a ranar Alhamis 13 ga watan Afrilu, inda kudinsa yanzu ya kai $210 da ba a taba samu ba a rana daya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A halin da ake ciki, dukiyar Elon Musk bata wuce $180bn, duk da kuwa ya samu kudin da suka kai $3.8bn.
Karin dukiyar Arnault ta faru ne sakamakon yadda kamfanoninsa na jaka; Louis Vuitton, na kayan shaye-shaye Moet & Champagne da kuma na turare Christian Dior suka samu ciniki mai tsoka.
Hannun jarin kamfanin ya tashi da 5.7% a kasuwar hannayen jarin Paris a ranar Alhamis din da ta gabata, inda aka ambaci kamfanin cikin manyan kamfanoni 10 na duniya.
Haka nan, kamfanin ya ci gaba da ganin kari har zuwa ranar Juma’a 14 ga watan Afrilu, inda ya karu da 0.7%.
Arnault ya shiga jerin attajiran da kudadensu suka taba haura $200bn
A halin yanzu, Arnault ya shiga sahun Elon Musk da Jeff Bezos a farkon watan nan, cikin jerin mutanen da suka taba hallakar kudin da suka kai $200bn, kuma shi ne na farko wanda ba dan Amurka ba.
Elon Musk da dukiyarsa ta taba kai $340bn ya samu tasgaru, inda kudaden suka ci gaba da sauka a yanzu. Kamfaninsa na mota Tesla na ci gaba da ja da baya a Amurka.
A bangarensa, Aliko Dangote, attajirin da ya fi kowa kudi a Afrika yanzu haka ya samu ribar $538m a rana daya, inda kudinsa yanzu suka kai $20.8bn.
An fara samun sabbin attajirai a jerin masu kudin duniya a wannan shekarar da muke ciki, alamu sun nuna arziki na kara yawa.
Asali: Legit.ng