Matan Jihar Kebbi Sun Ce Jam’iyyar ‘Tintsiya’ Ta Basu N3,000 Domin Su Zabe Ta a Zaben Asabar
- Jam’iyyar APC a jihar Kebbi ta raba wa mata kayan sayen baki a lokacin da ake ci gaba da cikon zaben gwamna a jihar
- Wannan na zuwa ne daidai lokacin da hukumar zabe ta INEC ta ce a karasa zaben jihar da aka fara a ranar 18 ga watan Maris
- Ba sabon abu bane ganin yadda ‘yan siyasa ke sayen kuri’un jama’a a zabukan kasar nan, musamman a wannan shekarar
Jihar Kebbi - Wata matar da ta zo kada kuri’a a cikon zaben yau Asabar a jihar Kebbi ta bayyana cewa, ‘yan jam’iyyar tsinsiya sun ba ta N3000, atamfa guda biyu da kwalin taliya domin ta zabe su.
Wata matar ta daban, ta ce jam’iyyar ta ba ta irin wadannan kayayyakin domin tabbatar da ta zabe su a zaben da ke gudana.
Wadannan matan sun zanta da gidan talabijin na Channels ne a Baban Dutsi Model Primary School da ke da rumfunar zabe uku; Karyo, Umijin Nana da Babban Dutsi.
INEC ta dakatar da wasu zabuka a Najeriya
A zabukan 25 ga watan Faburairu da kuma 18 ga watan Mayu, hukumar zabe ta ce bata amince da sakamakon da aka gabatar ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wannan kuwa ya faru ne sakamakon barkewar rikici da aka samu a zabukan biyu, inda ‘yan daba suka yi barna a jihohin Legas, Rivers, Adamawa, Taraba, Kebbi, Kano, Sokoto da dai sauransu.
A jihar Kebbi, jam’iyyar APC ta samu kuri’u 388,258 a zaben gwamna, inda jam’iyyar adawa ta PDP kuwa ta samu 342,980.
A wurin tattara sakamako, baturen zabe Farfesa Yusuf Sa’idu ya ce bai amince da sakamakon ba, don haka ya ayyana shi ‘inconclusive’.
Ya bayyana cewa, rikici, lalata kayan aikin zabe da kuma kawo tsaiko ga tsarin da hukumar zabe ta INEC ta samar ne dalilin soke zaben.
APC ta lashe sakamakon zaben sanata a jihar Yobe
A wani labarin, kunji yadda hukumar zabe ta ayyana Ibrahim Bomai a matsayin wanda ya lashe zaben sanatan Yobe ta Kudu a zaben bana.
Wannan na zuwa ne a zaben da aka karasa yau Asabar 15 ga watan Afrilun 2023, inda jama’a da yawa suka fito don kada kuri’unsu.
A halin da ake ciki, jihohi da yawa ne a Najeriya ake karasa zaben, ciki har da wasu yankunan jihar ta Yobe da ke Arewa maso Gabas.
Asali: Legit.ng