Daliban Jami'ar Gusau da Yan Bindiga Suka Sace Sun Shaki Iskar Yanci
- Bayan shafe kwanaki 12 a hannun masu garkuwa, ɗalibai mata na jami'ar tarayya Gusau sun kubuta
- Kungiyar dalibai ta jihar Zamfara ta tabbatar da dawowar Zainab da Maryam, waɗanda aka sace a gidan da suke zama a Sabon Gida
- Daliban sun yaba wa hukumar makaranta, hukumomin tsaro da ɗalibai maza da mata bisa gudummuwar da suka bayar
Zamfara - Ɗalibai mata 2 na jami'ar tarayya da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara, waɗanda suka shiga hannun masu garkuwa sun shaƙi isƙar 'yanci
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa ɗaliban, Maryam da Zainab, sun kubuta daga hannun 'yan bindiga bayan shafe kwanaki 12 a cikin Jeji.
Idan baku manta ba Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoto cewa an sance daliban ne yayin da wasu yan bindiga suka kutsa gidan kwanansu a kauyen Sabon Gida.
Ƙungiyar ɗaliban jihar Zamfara ta tabbatar da dawowar daliban amma ba ta ce komai ba kan ko an biya kuɗin fansa kafin su kubuta, kamar yadda Daily Trust ta rahoto..
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jami'in hulɗa da jama'a na ƙungiyar, Umar Abubakar, ya taya shugabannin jami'a murna da kuma iyayen ɗaliban, waɗanda Allah kaɗai ya san halin da suka shiga bayan sace 'ya'yansu.
"Mun yaba da babban murya da koƙarin jagororin makaranta da kuma jajircewar da suka yi wajen tabbatar da ɗaliban sun kubuta."
"Haka nan mun yaba da namijin kokarin hukumomin tsaron mu, waɗanda suka ba da gudummuwa ta kowace hanya ba tare da gajiya wa ba har aka samu kubutar da ɗaliban guda biyu."
"Muna ƙara jinjinawa yan uwa ɗalibai bisa Addu'o'in da suka yi, da ƙungiyar yan uwa ɗalibai mata bisa nuna sha'awa, haɗin kai da taimakawa aka kubutar da ɗaliban."
- Umar Abubakar
Bugu da ƙari, Abubakar ya kara da yin kira ga hukumomin tsaro su tabbata sun kama maharan da duk wanda ya ɗauki nauyinsu kuma a hukunta su domin guje wa sake faruwar haka nan gaba.
Legit.ng Hausa ta zanta da wani ɗalibin jami'ar da ke shekarar farko a karatunsa, ya tabbatar da dawowar ɗaliban guda biyu amma ya ce bai da tabbacin ko an biya fansa.
Ɗalibin wanda ya nemi a ɓoye bayanansa saboda halin tsaro, ya ce:
"Eh tabbas sun kubuta daga hannun masu garkuwan, amma yanayin da aka bi wajen sace su akwai alamun tambaya. Lokacin da aka ɗauke su ban dawo makaranta ba amma na je wurin da na dawo."
"Wato abinda ya faru kamar yadda wata ɗaliba dake zaune a gidan ta faɗa mana, da suka shiga gidan ba wanda suka taɓa, har haska Cocila suka yi suna diba lambar ɗakin ɗaliban."
"Wannan ya sa ake ganin dama aiko su aka yi kuma su biyun kacal suka ɗauka. Bayan faruwar lamarin matan sun ce ba zasu koma gidan ba, amma da aka kawo sojoji, hankalin ɗaliban ya kwanta sun koma kamar da."
Sojoji sun kashe yan bindiga 15
A wani labarin kuma Sojojin Najeriya Sun Ɗanɗana Wa Yan Bindiga Ɗacin Mutuwa, Sun Sheƙe da Yawa
Wasu mahara sun kwashi kashinsu a hannun Sojoji da yan banga, akalla yan ta'adda 15 suka sheƙa barzahu a jihar Zamfara.
Sojoji da haɗin guiwar yan banda sun kai ɗauki yayin da suka samu labarin yan bindiga sun shiga kauyuka biyu.
Asali: Legit.ng