Ana Tsaka Da Azumi Wani Abin Fashe Wa Ya Tashi a Birnin Dutse

Ana Tsaka Da Azumi Wani Abin Fashe Wa Ya Tashi a Birnin Dutse

  • Wani abin fashe wa da ake tunanin cewa bam ne ya tashi a cikin birnin Dutse na jihar Jigawa
  • Shaidun ganau ba jiyau ba sun tabbatar da tashin abin fashe war wanda bai ɗauki ran kowa ba
  • Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta ce tuni har ta fara gudanar da bincike kan lamarin

Jihar Jigawa - Wani abin fashe wa da ake kyautata zaton bam ne ya tashi a birnin Dutse, babban birnin jihar Jigawa.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa fashewar abin ta sanya mutanen birnin Dutse shiga cikin halin ɗar-ɗar.

Wani abin fashewa ya tashi a Jigawa
Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar
Asali: UGC

Fashewar abin a cewar shaidun ganau ba jiyau ba da kuma ƴan sanda, ya auku ne a yammacin ranar Talata akan layin Hakimi, cikin birnin Dutse, inda wani mutum ɗaya ya samu raunika.

Kara karanta wannan

Kano: Yan Sanda Sun Cafke Wasu Mutum 3 Bisa Tilasta Wani Almajiri Cin Bahaya Ana Azumi

Wani wanda abin ya faru akan idon sa mai suna Friday Frayo, ya bayyana cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Na ɗauki wani abu cikin wata baƙar leda a tunani na wani abu ne da na aje a wajen, amma sai naga wata na'ura tana harbawa cikin sauri, nan da nan na jefar da ita."
"Ina jefar da ita kawai sai na'urar ta fashe, hakan ya sanya na samu raunika daga ɓurɓushin fashewarta."

Frayo ya bayyana cewa babu wanda ya rasu a fashewar abin, sai shi kawai da ya samu raunika da kuma wani allon sanarwa da ya lalace a kusa da shagon sa.

Ƴan sanda sun tabbatar da aukuwar lamarin

Da yake tabbatar da rahoton, kakakin rundunar ƴan sandan jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam, ya bayyana cewa fashewar abin ta auku ne da misalin ƙarfe 7:40 na dare a ranar Talata, cewar rahoton Daily Post

Kara karanta wannan

An Gurfanar Da Wani Magidanci Mai Auren Mata 5 A Kotun Musulunci, Alkali Ya Zartar Masa Hukunci

Ya bayyana cewa ƴan sanda na gudanar da bincike kan lamarin domin gano abinda ya haddasa fashewar da kuma irin na'urar da ta fashe.

Shiisu ya kuma shawarci mutanen jihar da su riƙa kula sosai idan suna cikin cunkoson jama'a sannan su kawo rahoton duk wani abu da ba su gamsu da shi ba.

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani mazaunin birnin Dutse na jihar Jigawa, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin.

"Eh tabbas lamarin ya auku a layin Hakimi bayan sallar Isha'i." A cewar sa

Wani mai suna Shamsu ya tabbatar da aukuwar lamarin amma ya ce bai je wurin da lamarin ya auku ba.

"Eh tabbas na ji ance wani abu ya fashe amma gaskiya lokacin ina shago ina ɗinki ban je wurin ba."

Sojoji Sun Kai Sumame Sun Rufe Wasu Gidajen Magajiya a Borno

A wani labarin na daban kuma, sojoji sun kulle wasu gidajen karuwai da ke a cikon birnin Maiduguri na jihar Borno.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Bene Mai Hawa 7 Ya Rushe, Ya Danne Danne Mutane da Yawa Ana Cikin Azumi

Sojojin sun kulle gidajen ne a wani sumame sa suka kai a yankin da gidajen karuwan suke.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng